Amurka na kara jibge manyan motoci masu sulke da makamai a sansanoninsu na Hasaka dake Syria

 


- Sojojin mamaya na Amurka na kara kawo motocin soji da kwantena da suka fito daga arewacin Iraki zuwa sansanonin su na  Syria ta hanyar haramtacciyar hanya ta al-Walid da ke yankin Hasaka.


Wani ayarin motocin mamaya na Amurka da ya kunshi motoci 60 da suka hada da manyan motoci makare da kwantenan makamai da alburusai da manyan motocin yaki na soja baya ga tankokin yaki 40 na satar mai tare da rakiyar motocin soji uku, sun shiga yankunan Siriya ta haramtacciyar hanya ta Al-Walid. 


Kamar yadda majiyoyin gida daga yankin al-Yarubiya da ke Hasaka suka shaida wa wakilin SANA.


Majiyar ta kara da cewa ayarin motocin sun nufi garin al-Yarubiya, inda suka fito daga sansanonin 'yan mamaya a kasar Iraki, daga nan kuma ayarin suka nufi sansanonin 'yan mamaya na kasar Siriya.


Kayayyakin da aka yi jigilar su a cikin motocin ana aika su ne domin tallafawa mayakan na QSD, da kuma baiwa kungiyoyin 'yan ta'adda makamai a kusa da sansanonin mamayar Amurka da ke yankin Al-Tanf da ke gabashin gabashin Homs, da suke amfani da su wajen kai hare-hare akan gine-ginen zama, abubuwan more rayuwa na jihar, da kuma wuraren da Sojojin Larabawa na Siriya suke.


Bushra Dabin/Ruaa al-Jazaeri ce ta hada wannan rahoto, Mahadi Tukur Almizan ya fassara maku

Post a Comment

0 Comments