- Mahadi Tukur Almizan
Dakarun Mamaya na “Isra’ila” Sun kashe wani matashi Bafalasdine ya a lokacin da suka Kai hari kudancin birnin Bethlehem da ke Yammacin Kogin Jordan.
Kamfanin dillancin labaran Wafa na kasar Falasdinu ya bayyana cewa, an kashe Bafalasdine dan shekaru 16 da haihuwa mai suna Mustafa Amer Sabbah a ranar Juma'a ta hanyar bude wuta daga jami'an haramtaciyar kasar "Isra'ila" a lokacin arangama da ta barke a kauyen Tuqu da ke kudu maso gabashin Bethlehem.
Kamfanin dillancin labaran ya kara da cewa, "An yi arangama a yammacin kofar shiga kauyen Tuqu, inda sojojin mamaya na 'Isra'ila' suka harba harsasai masu rai, da barkonon tsohuwa, da gurneti a kan mazauna kauyen, inda suka yi harbi tare da raunata wani matashi a kirji."
An garzaya da Sabbah asibiti cikin mawuyacin hali sakamakon harbin da aka yi masa a kirji, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Kamfanin dillancin labaran Shehab na kasar Falasdinu shi ma ya bayar da rahoton faruwar lamarin, inda ya kara da cewa dakarun na HKI sun rufe kofar yammacin kauyen da wani shingen bincike bayan an tabbatar da mutuwar matashin.
Mummunar harbin ya zo ne kwana guda bayan da sojojin HKI din suka kashe wani Bafalasdine a tsakiyar yankin yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye kan zargin daba wuka da kuma bankade Sojojinsu da mota.
An harbe mutumin mai suna Ahmad Yaqoub Taha mai shekaru 39 a duniya a kusa da haramtacciyar matsugunan Ariel da ke kusa da birnin Salfit na Falasdinu, inda a wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce ya yi kokarin kutsawa kan sojoji. wadanda suke a wata mahada a yankin.
A cikin watannin da suka gabata, kungiyar "Isra'ila" ta zafafa kai hare-hare kan garuruwan Falasdinawa a cikin yankunan da ta mamaye.
Sakamakon wadannan hare-hare, Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da yin garkuwa da wasu da dama.
Galibin hare-haren dai sun fi mayar da hankali ne kan garuruwan Nablus da Jenin da ke gabar yammacin kogin Jordan, inda dakarun HKI ke kokarin dakile yunkurin da Falasdinawan ke yi na adawa da mamayar da suke yi.
Akalla Falasdinawa 106 ne dakarun HKI suka kashe a wannan shekarar, ciki har da wata tsohuwa mace da akalla yara tara, a cewar Wafa.
0 Comments