Gwamnatin Sahayoniya ta kaddamar da hare-hare ta sama a lardin Homs na kasar Siriya, inda suka raunata akalla sojoji 5 a cewar ma'aikatar tsaron kasar ta Siriya.
Gwamnatin Isra'ila ta kaddamar da wani hari ta sama daga arewa maso yammacin Beirut inda ta kai hari kan wasu matsugunan birnin Homs da kauyukanta da misalin karfe 00:35 na safe (21:35 agogon GMT), in ji ma'aikatar tsaron kasar ta Syria a cikin wata sanarwa da ta fitar ta kafar yada labaran kasar.
Jami'an tsaron sararin samaniyar Siriya sun kakkabe makaman masu linzami tare da harbo wasu daga cikinsu.
Majiyar sojan Syria ta bayyana a kafar yada labaran kasar cewa, hare-haren sun yi barna tare da jikkata wasu sojoji biyar, kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.
Sojojin gwamnatin Isra'ila sun ki cewa komai kan rahoton.
Wasu majiyoyin leken asirin kasashen yammacin duniya guda biyu da suka bukaci a sakaya sunansu sun shaidawa kamfanin dillancin labaran reuters cewa, an kai harin ne a sansanin sojin sama na T4 dake yammacin tsohon birnin Palmyra, da kuma filin jirgin saman al-Dabaa dake kusa da birnin al-Qusayr dake kusa da kan iyakar kasar Lebanon.
Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai a watan da ya gabata a kan tashar jirgin saman Aleppo ya sa ya daina aiki na tsawon kwanaki biyu.
Filin jirgin ya kasance babban hanyar jigilar kayan agaji tun bayan girgizar kasa mai karfin awo 7.8 da ta afku a Siriya da Turkiyya a ranar 6 ga watan Fabrairu.
0 Comments