- Falasdinawa da dama ne suka jikkata yayin da sojojin mamaya na Isra'ila suka mamaye birnin Hebron da ke gabar yammacin kogin Jordan a safiyar yau Laraba.
Dakarun mamaya sun kutsa cikin garin Beit Amer da yankin Asida da Ras al-Jawhra da ke kofar arewacin birnin, inda suka harba bama-bamai masu guba kan Falasdinawa, lamarin da ya yi sanadin raunata daya daga cikinsu, baya ga wasu da dama da suka kamu da matsalar shakar iska. kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ruwaito.
Falasdinawa 12 sun sha fama da shakewa yayin da sojojin mamaya na Isra'ila suka mamaye garin Beita da ke kudancin Nablus a gabar yammacin kogin Jordan.
A gefe guda kuma, Falasdinawa da dama ne suka gudanar da zanga-zanga, a garuruwan Hebron da Nablus, domin yin tir da harin da dakarun mamaya suka kai a Masallacin Al-Aqsa, da kuma laifukan mamaya da suka aikata a kan Falasdinawa, musamman a birnin Kudus.
Rafah al-Allouni/Hala Zain
0 Comments