GOYON BAYAN PALASDINAWA A LONDON | Masu zanga-zanga a London sun bukaci a kawo karshen cin zarafin Falasdinawa

 



 – Daruruwan masu zanga-zanga ne suka taru a gaban ofishin jakadancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a birnin Landan a ranar Juma’a domin yin Allah wadai da hare-haren baya-bayan nan da aka kai a masallacin Al-Aqsa da ke gabashin birnin Kudus tare da yin kira da a kawo karshen hare-haren da Isra’ila ke kaiwa.


Masu zanga-zangar sun yi sahu a kan titunan babban birnin kasar, rike da tutoci da kuma alamomin "Free Palestine" da "#HandsoffAlAqsa".


"Suna tsorona adalci, suna tsoron  gaskiya, komai yawan karyar da suke yi muku ta kafafen yada labarai na BBC da Amurka," in ji wani mai zanga-zangar. "Lokacin Isra'ila  mai zalunci ya kusan zuwa ƙarshe."



Ana ci gaba da zaman dar-dar a birnin Quds, tun bayan da sojojin Isra'ila suka kai wa masu ibada hari a harabar masallacin al-Aqsa cikin dare a ranar Larabar da ta gabata a cikin watan Ramadan.


Harin da aka kai a masallacin mai tsarki ya yi sanadin jikkata Falasdinawa akalla 12.


An ci gaba da kai farmakin har zuwa safiyar ranar Alhamis, yayin da aka sake ganin sojojin Isra'ila suna farma Falasdinawa da korar Falasdinawa daga harabar tare da hana su yin addu'a. 


Akalla Falasdinawa 400 ne aka kama a ranar Laraba kuma suna ci gaba da kasancewa a hannun Isra’ila, a cewar jami’an Falasdinawa. Ana tsare da su ne a ofishin 'yan sanda da ke unguwar Atarot da ke Gabashin Quds da aka mamaye.


Shaidu na Falasdinawa sun ce sojojin Isra'ila sun yi amfani da karfi fiye da kima, da suka hada da gurneti da hayaki mai sa hawaye, lamarin da ya janyo raunata masu ibadar, da kuma dukansu da sanduna da bindigu.

Post a Comment

0 Comments