Gwarzon Falasɗinu: Dakta Fatihi Shaqaqi.

 



©Baqeer 


Asalinsa haifaffen zirin Gazza ne, an haifi Dakta Fatihi ne a shekarar 1951, ya yi karatun lissafi (Mathematics) da likitanci bangaren yara kanana (Pediatrics) a jami'o'i a kasar Falasdinu da a kasar Masar. Ya tasirantu matuka da gwagwarmayar Imam Hassan al-Banna da Sayyid Qutb 'yan Ikhwan, sannan Shahid Ahmad Yassin da ya assasa Hamas shi ma ya mishi tasiri. 


Amma mutumin da ya fi mishi tasiri a rayuwarshi, Imam al-Khomeini (QS) ne, juyin-juya halin Musulunci a Iran shi ne babban abinda ya kara wa Dakta Fatihi karfin gwiwa har ya assasa 'Harakat al-Jihād al-Islāmi fi Filastīn' wato Harkar Jihadi a Falasdin, wacce ya yi mata tsari irin na juyin-juya halin Musulunci na Iran wanda Imam al-Khomeini ya jagoranta; a cewarshi ya gane gwagwarmayar Musulunci ce kawai mafita ga al'ummar Falasdinu kamar yadda Imam al-Khomeini ya yi, duk kuwa da cewa Dakta Fatihi ba dan Shi'a bane.


Haramtacciyar kasar isra'ila ta dade ta na hakon Dakta, wanda hakan ya tursasa mishi komawa kasar Syria da rayuwa, basu samu nasarar kashe shi ba a sai a kasar Malta, a shekarar 1995; kwanaki kadan bayan ya bar kasar Libiya, inda wasu jami'an leken asirin Mossad suka shahadantar da shi ta hanyar harbinsa sau biyu a goshi, da kuma sau 4 a bayanshi. Su Dakta suna daga cikin kalilan din da jininsu zai hana isra'ila wanzuwa a doron kasa. Allah ya kara kusanto mana da wargajewar isra'ila da dukkan azzaluman duniya.

Post a Comment

0 Comments