– Hadaddiyar Daular Larabawa ta fara ficewa daga kasar Yemen a hukumance, a cewar Mohammed Al-Bukhaiti, wani jigo a kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen kuma gwamnan lardin Dhamar.
Al-Bukhaiti ya sanar da cewa "akwai fahimtar juna da Saudiyya" dangane da kasar Yemen ba tare da bayyana cikakken bayani ba.
A wata hira da ya yi da Al-Mayadeen, Al-Bukhaiti ya bayyana cewa "hadin Kan da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi da Saudiyya wajen kai hari kan Yaman babban kuskure ne, kuma ya kamata UAE ta koyi darasi sannan ta janye gaba daya."
Al-Bukhaiti ya jaddada cewa, duk wani yunkuri da Saudiyya za ta yi na samun zaman lafiya da kasar Yemen zai karfafa matsayin Saudiyya.
A halin da ake ciki kuma, Saudiyya da Oman na neman kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a Yaman. A cikin kwanaki biyu masu zuwa ne ake sa ran tawagar kasar Saudiyya karkashin jagorancin Mohammed Al-Jaber tare da rakiyar tawagar kasar Oman za ta isa babban birnin kasar Sanaa, domin tattaunawa kan yadda za a sake bude tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama na kasar Yemen baki daya, da biyan albashin ma'aikatan gwamnati.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, idan aka cimma matsaya, bangarorin na iya sanar da ita kafin hutun sallar idin da zai fara a ranar 20 ga watan Afrilu.
A cewar Al-Bukhaiti, sharuddan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta sun sha bamban da na samar da zaman lafiya. Ya bayyana cewa, "Yarjejeniyar tsagaita bude wuta kafin sallar Idi za a yi ta ne a matakai biyu." Ya kuma yi kira ga 'yan kasar Yemen da ke da hannu a cikin hare-haren wuce gona da iri da kada su rasa wannan damar.
A halin da ake ciki kuma, za a ci gaba da kokarin kawo karshen hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen da kuma kawar da mamayar da aka yi mata ta hanyar tattaunawa, a cewar Mohammed Abdul Salam, kakakin kungiyar Ansarullah ta Houthi kuma shugaban tawagarsu ta tattaunawa. "In Allah ya yarda, yunkurin zai kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya wadda za ta biya bukatun al'ummar Yemen daga Sa'ada zuwa Mahra," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Abdulwahab al-Mahbashi, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah, ya jaddada cewa "yarjejeniyar Iran da Saudiyya na da kyau kuma za ta yi tasiri ga ƙasar ta Yemen."
An kuma bayar da rahoton cewa, Riyadh ta sanar da majalisar shugaban kasar shawarar da ta yanke na kawo karshen yakin da kuma "rufe fayil din Yemen din."
0 Comments