Hare-haren Jiragen saman Isra'ila a zirin Gaza na ranar Juma'a

 


  - Jiragen yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun fara kai hare-hare a zirin Gaza da sanyin safiyar Juma'a, bayan da Firaminista Benjamin Netanyahu ya zargi kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas da kai harin roka a ranar Alhamis daga yankin Lebanon.


Sojojin Isra'ila sun wallafa a shafinsu na twitter da karfe 12:21 na safe agogon kasar cewa sojojin gwamnatin suna " kai hare-hare a Gaza a halin yanzu".


Kafofin yada labaran Falasdinu sun ruwaito cewa, an fara aikin tsaron sararin samaniyar Hamas. 


Kawo yanzu dai babu rahoton asarar rayuka. Hotunan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna fashewar abubuwa masu haske a daren.


Babu wanda ya dauki alhakin kai harin da aka kai a Isra'ilan, amma sojojin Isra'ila sun zargi kungiyar gwagwarmayar Hamas a Gaza.


Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce harin shi ne mafi muni tun shekara ta 2006, lokacin da Isra'ila ta yi yunkurin kawar da kungiyar Hizbullah daga kudancin Lebanon. Wannan yakin dai ana daukarsa a matsayin nasara ga Hizbullah.


Kafofin yada labaran kasar na cewa, Hamas da Hizbullah sun ajiye makamansu masu cin dogon zango a cikin shirin ko-ta-kwana, kuma za su iya kai hari kan yankunan da suka mamaye a matsayin martani ga harin bam da sojojin Isra'ila suka kai.


An ba da rahoton cewa an dawo da dukkan sojojin Isra'ila daga hutu, kuma an sanya su  a sassan da ke kusa da kan iyaka da Lebanon a cikin shirin ko-ta-kwana a ranar Alhamis.


Kafofin yada labarai a birnin Tel Aviv sun yi hasashen cewa an kai hari a Gaza, yayin da akwai yiwuwar wani farmaki a Lebanon.


A farkon makon nan ne 'yan sandan Isra'ila suka kai hari tare da kame daruruwan Falasdinawa a masallacin Al-Aqsa, lamarin da ya kawo cikas ga ayyukan ibada a cikin watan Ramadan. 


Wasu Falasdinawa sun yi tururuwa zuwa masallacin bayan rahotannin da ke cewa wasu 'yan Isra'ila sun mamaye harabar masallacin.


A makon da ya gabata ne Netanyahu ya fuskanci gagarumar zanga-zangar da 'yan adawa masu sassaucin ra'ayi suka shirya, wadanda suka bukaci ya yi murabus saboda shirin yin garambawul a kotun kolin Isra'ila.

Post a Comment

0 Comments