HASSAN NASRULLAH Shugaban kungiyar Hizbullah ya gana da jami'an Hamas danganeda al'amarin Palastinu.

 


 - Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyed Hassan Nasrallah, ya gana da manyan jami'an Hamas a birnin Beirut, yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar a yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye, musamman  a harabar masallacin Al-Aqsa.


Tawagar ta hada da Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa, Sheikh Saleh al-Arouri, mataimakin shugaban ofishin siyasa, da manyan jami'ai Khalil al-Hayya da Osama Hamdan, kamar yadda kafafen yada labaran Falasdinu suka ruwaito.


Taron dai ya mayar da hankali ne kan sabbin batutuwan da suka shafi yanayinda ake ciki a Falasdinu, Labanon, da kuma Gabas ta Tsakiya.


Sun tattauna batutuwan baya-bayan nan a zirin Gaza, da yammacin kogin Jordan, da kuma al-Quds.


Sayyid Nasrallah ya yi gargadi ga Isra'ila kan yadda gwamnatin kasar ke ci gaba kai hare-hare a harabar masallacin al-Aqsa da ke birnin Quds da ta mamaye.


Har ila yau, Al-Quds Brigades, reshen soji na kungiyar gwagwarmayar Islama ta Palasdinawa, sun yi Allah wadai da farmakin baya bayan nan da dakarun haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan masu ibada a masallacin al-Aqsa.


Kungiyar ta ce harin "Jan layi" ne ga dukkan Falasdinawa. 


Abu Hamza mai magana da yawun kungiyar ya ce za su ci gaba da tinkarar zaluncin gwamnatin sahyoniyawan kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da ayyukan ramuwar gayya ta kowace hanya.


Kungiyar Kata’ib Hezbollah da kungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta Yaman sun bayyana goyon bayansu ga Falasdinawan sakamakon kutsawa da hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suke yi. 


Kungiyar Hizbullah Kata'ib ta yi kira ga daukacin al'ummar musulmi da su tashi tsaye wajen yakar kutsen Isra'ila tare da kare masallacin al-Aqsa ta dukkan hanyoyin da suka dace.


Har ila yau kungiyar ta Ansarullah ta bayyana cewa, za ta bada duk wani nau'i na goyon baya ga kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinawa da kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon domin tunkarar sojojin Isra'ila kan munanan farmakin da ta kai kan masallacin Al-Aqsa.


Ministan harkokin soji na Isra'ila Yoav Gallant ya bayyana cewa, gwamnatin kasar a shirye ta ke ta kowane fanni na sake kai wani sabon hari.


Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana kaduwa da damuwa game da kutsen da sojojin Isra'ila suka yi a cikin masallacin, ya kuma ce, "Wajen ibada ya kamata a yi amfani da su ne kawai don gudanar da bukukuwan addini cikin lumana."

Post a Comment

0 Comments