Ma'aikatar tsaron Siriya ta sanar da cewa na'urorin tsaronta na sama sun harbo rokokin "Isra'ila" da dama a kudancin kasar.
An fara luguden wuta a Siriya da misalin karfe 5:00 na safe agogon kasar a ranar Lahadin da ta gabata kuma ya yi barna.
A cewar ma'aikatar tsaron, Rundunar tsaron saman Siriya ta harbo wasu rokoki na "Isra'ila" da aka harba daga tuddan Golan zuwa wurare da dama a kudancin Siriya.
Tun da farko, wani gidan yada labarai na kasar Syria ya ba da rahoton fashewar wasu abubuwa a kusa da Damascus cikin dare.
Yayin da ba a fayyace musabbabin fashewar ba, rundunar sojin Isra'ila ta ce an harba rokoki da dama daga wajen Syria zuwa tuddan Golan na Isra'ila.
Harin farko ta harba makaman roka mai harsashi uku a ranar Asabar, inda wasu rokoki uku daban suka biyo baya a safiyar Lahadi.
Sojojin "Isra'ila" sun yi zargin cewa daya daga cikin rokoki uku na farko ya tsallaka cikin yankin da suka kira "Iyar ikon Isra'ila" kuma ya fado a budadden wurare a kudancin tuddan Golan."
0 Comments