KU SAN WANI ABU DAGA RAYUWAR IMAM HASSAN BIN ALIY A.S


 


Aliyu Samba


Imam Hassan ɗa ne ga Imamu Ali ɗan abi talib, kuma ɗa ga Nana Faɗima ƴar shugaban Halitta Annabi Muhammad ﷺ. An haife shi a ranar 15 ga watan Ramadan shekara ta 3 bayan hijira, wacca tayi daidai da 1 ga watan Disamba, 624 Miladiyya.


Imam Hassan shine ɗa na farko wajen Imam Ali da Nana faɗima, kuma wanda makarantar Ahlussunnah suke ƙirgawa a mutum na 5 cikin Khulafa'ur rashidin, a wajen Mabiya Mazhabar shia ta ahlul baiti kuma yake a matsayin Imami na 2 cikin jerin Imaman shiriya 12. 


Imam Hassan ya zama Khalifa bayan wafatin mahaifin sa Imam Ali na tsawon wata shida kafin Mu'awiyya dan Abi sufyana ya mayar da tsarin khilafa mulki tare da kutunguilar daya daga gwamnonin sa Mugira ɗan Shu'uba, daga kansa ne aka fara mulki na baƙin zalunci a tarihin musulunci.


Imam Al-Hasan ya kasance mutum mai yawan taimako, mai kyawawan dabi'u, mai hikima da ilimi, haƙuri juriya da kuma sadaukantaka. Yayi rayuwarsa a garin Madina har zuwa wafatinsa, ya rasu yana da shekaru 45 kuma an binne shi a maƙabartar Jannatl Baqi dake Madina. 


Matarsa Ja’ada ƴar Ash’as dan ƙais ce wacca tarihi ya nuna cewa ita ce sanadiyyar shahadar Imam Hassan sakamakon guba da ta shayar dashi. Dalilai wadanda suka fi ƙarfi daga ɓangaren mazhabar Ahlul Baiti sun bayyana cewa Mu'awiyah ne ya sufurci matar Imam Hassan tayi masa wannan ɗanyen aiki na kashe ɗan Manzon Allah SAWA, tare da yi mata alƙawarin zai aura mata ɗan sa Yazidu dan ta zama Ya-kumbo a gidan da suka kira gidan khilafa a wannan lokacin. 


Wasu masu bincike kan sha'anin addinin musulunci masu suna Madelung da Donaldson cikin wani littafi Mai suna ''The Shi'ite Religion: A History of Islam in Persia and Irak'' bugun Burleigh Press a shafi na 66–78 sun kawo wasu hujjoji da ke nuna cewa wata daga matan Imam Hassan wacca take ɗiya ga Suhail bin Amr ce ta bashi guba, ko kuma daya daga masu yi masa hidima, suna ƙarfafar wannan ra'ayi da littafan tarihi na Waƙidi da kuma Al-Mada'ini. Shi Madelung ya na kan cewa an juya tarihin waƙi'ar ne saboda yadda musulmi suka damu da sha'anin wafatin Imam Alhassan.


Wasu riwayoyi sun nuna cewa Imam Hassan bai bayyanawa dan uwan sa Imam Alhussaini wanda ya/ta kashe shi ba saboda gudun kada hukunci ya sauka akan wanda ba a da tabbacin shi ya aiwatar da hakan gareshi, a lokaci guda kuma ruwayoyi daga dukkan bangarorin shia da Sunnah sun hadu akan cewa Ja’adatu ce ta kashe Imam Hassan da guba. 


Imam Hassan Yana da shekaru 38 a lokacin da Mu'awiyah ya amshi khilafa daga hannun sa, a lokacin Mu'awiyah yana shekara 58. Saboda shekarun Mu'awiyah da suka ja ya sanya ya maida ɗan sa Yazidu ya zama Waliyyul Amri a bayansa, wanda hakan ya saɓa da ƙa'idar da Imam Hassan ya shimfida kafin ya sakar wa Mu'awiyah abinda ya karɓa daga gareshi, a yadda shi Mu'awiyah ya zata shine tazarar shekaru dake tsakanin sa da Imam Hassan zai sa ya riga shi mutuwa, wanda wannan na daga dalilan da ke ƙarfafar ra'ayin cewa da sa hannun sa aka kashe Imam Hassan A.S.


Binne Imam Hassan a tare da Kakansa Annabi Muhammad SAWA ya zama wata matsala mai girman gaske a wannan lokaci wadda ta so ta bayu ga zubar da jini kamar yadda ruwayoyin Shia suka bayyana, Imam Hassan ya umarci dan uwan sa Imam Hussain da ya binne shi kusa da kakansa Annabi Muhammad SAWA muddin ba wata fitina aka ga zata auku ba. Gwamnan Madina ƙarƙashin mulkin Banu Umayyah mai suna Sa'id Binl Aas bai tsoma baki wajen hanawa ba, amma marwanu yayi rantsuwa cewa bazai bari a binne Alhassan a kusa da Manzon Allah SAWA ba da Abubakar da Umar, saboda cewar sa Usman an binne shi a Maƙabartar Baqi'ah.


Banu Hashim da Banu Umayyah sun so su yi yaƙi a wannan lokacin kamar yadda yazo a wani littafi Mai suna ''The succession to Muhammad'' da bayanin cewa Abu Huraira wanda ya goyi bayan Mu'awiyah a lokacin Siffin, ya bayyana wa Marwan irin matsayin da Alhassan da Alhussaini suke dashi wajen Manzon Allah SAWA. Marwan bai gamsu ba, haka Nana A'isha ma a wannan lokacin bata goyi bayan binne Alhassan tare da Annabi SAWA ba. 


An ruwaito tana cewa: ''Dakin nawa ne, kuma bazan bari a binne kowa a cikin sa ba'' (cikakken bayani ya cikin littafin ''The Religious Roots of the Syrian Conflict'' shaf na 68). An samu sabani sosai tsakanin Sahabbai akan wannan waqi'a, ibn Abbas yana daga waɗanda sukai suka ga Nana A'isha akan wannan matsayar da kuma hawan raƙumi da tayi dan yaƙi da mahaifin Alhassan a ''jamal''.


Rashin yardar da tayi a binne Alhassan tare da Annabi bayan ta bari an binne mahaifin ta Abubakar da Umar kusa da SHI yana daga dalilan da suka sosa zuƙatan mabiyan Imam Ali AS. Muhammad ibnl Hanafiyya Yana daga waɗanda suka lallashi Imam Hussain da tuna masa fadin Imam Hassan na cewa ''Idan anji tsoron fitina a binne shi a Baqi'ah'', ya ce da Imam Hussain ''wacce Fitina ce zata kai Musulmi su zare takobi ga ƴan uwansu musulmi?''


Daga nan ne aka binne Imam Hassan a Baqi'ah wanda Imam Hussain ya jagoranci sallar sa aka binne shi. A shekara ta 1925, an rushe hubbaren inda aka binne Imam Hassan a lokacin bullar wahabiyyanci da kwace ikon garin Makkah da sukai, a lokacin an rushe wuraren tarihin musulunci da dama a Makkah da Madina tare da tuhumar cewa bidi'a ne da kuma shirka.


Imam Hassan ya yi wafati ya bar mata kamar haka:

Umm Kulthum bint al-Fadl bin al-Abbas

Khawla bint Manzoor

Umm Bashir bint Abi Mas'ud al-Ansari

Ja'da bint al-Ash'at (Wacca aka zarga da bashi guba)

Umm Ishaq bint Talha bin Ubaydullah

Umm Farwa


Sannan ya bar ƴaƴa kamar haka: 

Al-Hasan al-Muthana

Qāsim

Muhammad ibn Hasan

Abu Bakr ibn Hasan

Fātimah

Ummul Khair

Umm Salma

Ummul Hasan

Zayd Abu'l-Ḥasan

Zayd

Abdullah

Talha

Maymūnah

Beshr

Umm al-Husayn


Allah ya ƙara tsira da aminci ga ruhin Imam Alhassan, Allah ya ƙara narkon azaba ga makasan sa da masu goyon bayan zaluncin da akai masa. 


https://aliyusamba.wordpress.com/2021/04/27/ku-san-wani-abu-daga-rayuwar-imam-hassan-bin-aliy-a-s/


©Aliyu Samba

27/04/2021

Post a Comment

0 Comments