MARTANI AKAN HARE-HAREN ISRA'ILA GA PALASDINAWA | "SUDAN ANONYMOUS" SUNYI KUTSE A KAFAFEN YANAR GIZON ISRA'ILA

 



Daya daga cikin manyan kamfanonin tsaro na yanar gizo na Sahayoniya (Check Point) wasu gungun masu kutse da suka kira kansu "Sudan Anonymous" sun kwace ikonsu a ranar Talata da yamma.


  Ankwace ikon dayawa daga shafukan jami'o'in kasar ta Isra'ila, wannan kutse dai duka "Sudan Anonymous" ne sukayi


Daga cikin gidajen yanar gizon da akayima kutsen   sun haɗa da rukunin yanar gizon 'Tel Aviv University,’  ‘Hebrew University of Jerusalem,’ ‘Ben-Gurion University of the Negev,’ ‘Haifa University,’ ‘Weizmann Institute of Science,’ ‘Open University of ‘Israel’’ dakuma ‘Reichman University.'


Kungiyar ta wallafa wata sanarwa a shafinta na Telegram, inda ta lissafa wuraren da ta kai hari Wanda suka haɗa da "Kamfanonin ababen more rayuwa musamman Jami'o'in  'Isra'ila saboda abin da suke yi a Falasdinu.


Kungiyar ta kara da cewa wannan ba shine babban harin ta ba, babbar harin natafe, zai faru a ranar 7 ga Afrilu. 


Kamfanin tsaro na Intanet Radware ya bayyana cewa, ana yawan kai hare-hare ta yanar gizo kan al'ummar Sahayoniya a kowace shekara a ranar 7 ga Afrilu har tsawon shekaru goma dasuka gabata. 


Kamfanin a ranar Talata ya kuma gano harin da aka kai a gidajen yanar gizo,asibitoci, jaridu, matatun mai da sauransu.


Wannan harin wani bangare ne na wani kamfen da ake kira ‘OPIsrael’, inda masu fafutuka ke kokarin kai hari a kan intanet na ‘Isra’ila’, a cewar Ynet News. An rsake samun wasu daga cikin wuraren da aka kai hari ranar Talata.

Post a Comment

0 Comments