Yau 14 ga watan Ramadan , rana ce ta tunawa da shahadar jarumi Mukhtar Assaƙafi .
TAƘAITACCEN TARIHINSA
Shine Al-Mukhtar ɗan Abi Ubaid Assaƙafi . An haife shi a shekara ta 1 bayan hijira wato shekara ta 622 miladiyya . Ya rasu a shekara ta 67 bayan hijira watau shekara ta 686 miladiyya .
Mahaifiyarsa itace : Dumatu ƴar Wahb ɗan Umar , ƴar uwarsa kuwa sunanta Safiya bint Abi Ubaid, mata ga Sahabin Annabi (saww) Abdullahi ɗan Umar .
An binne shi a masallacin Kufa kusa da ƙabarin Muslim bn Aqeel (a.s.) , daura da hani bin Urwa , inda masallacin Imam Ali (a.s.) yake , ta bayan gidansa na Kufa .
Ya zauna a garuruwa da dama da suka haɗa da Ɗa'if, Madina, Al-Mada'in, Al-Lafqa, Kufa da Makkatul Mukarrama . Ana kuma masa laƙabi da Abu Ishaq, Kais, da kuma Yadullahi .
MATANSA DA ƳAƳANSA
Ya auri Ummu Thabit 'yar Samratul Fazariya , da Amra ƴar Annu'uman bin Bashir al-Ansari.
Ya'yansa kuwa sune : Ishaq da Thabit .
Yayi mubaya'a ga Imam Hasan Almujtaba (a.s.) a shekara ta 40 Hijiriyya bayan shahadar Imam Ali (a.s.) .
MOTSINSA DA DAULARSA
Cikin shekara ta 60 bayan hijira, aka ɗaure shi bayan sauke sirikinsa Annu'uman bin Bashir Al-Ansari daga Gwamnan Kufa, aka nada Ubaidullahi bin Ziyad a madadinsa , wanda a lokacin ne aka kashe Imam Hussain shi kuma Mukhtar yana tsare a gidan yarin .
Bayan an sake shi , ya yi aiki a wani yunkuri na ɗaukar fansar wadanda suka kashe Imam Husaini (a.s) , kuma hakika ya yi nasara a kan hakan , sannan ya ɗauki fansa kan wadanda suka kashe Imam Husaini (a.s.) , ta inda yabi ya dinga kashe masu hannu a kashe Imam Hussain (a.s.) , kamar su Umar bin Sa'ad bin Abi Waqqas, Ubaidullahi bin Ziyad bin Abihi , Shamru bin Zhil Jaushan, Harmalatu bin Kahil da sauransu.
Ya kafa daular Alawiyyawa a birnin Kufa wacce ta fadi a hannun rundunar Abdullahi bin Zubair , ƙarkashin jagorancin ɗan uwansa Mus'ab binil Zubair .
Kuma Al-Mukhtarus Saƙafi ya yi shahada ne a ranar 14 ga watan Ramadan shekara ta 67 Hijiriyya , shekara shida kenan bayan kashe Imam Hussain (a.s.) .
SAƁANIN MALAMAI AKANSA
Dangane da makomarsa kuwa an samu karo da saɓanin Ruwayoyi akan hakan , wasu Riwayoyin suna bayyana kyakkyawar makomarsa da kasancewarsa mutumin kirki Salihi, wasu kuma ruwayoyin akasin haka ne , suna sukarsa tare da nuna shi a matsayin mai gurɓatacciyar Aƙida musamman ma dai mas'alar kafa Daularsa an kai ruwa rana akanta tsakanin Malamai .
Saɓanin Waɗannan Ruwayoyin yasa Malamai suka kasu gida Uku akan sha'anin Mukhtar:
1. Wasu suka sanya shi daga cikin Salihan bayi mutumin kirki da ya taimaki Ahlul baiti (a.s) bayan sun iya rinjayar da Ruwayoyin dake yabonsa da raunana Riwayoyin da suke sukarsa da dalililai mabanbanta , kamar yanda Sayyid Khu'i (Rahimahullah) a cikin "Mu'ujam "yace : Riwayoyin da suke sukar Mukhtar suna da rauni sosai , sannan masu yabonsa sunfi yawa , shi yasa wannan ne ra'ayin mafi yawan Malaman Shi'a akansa cewa yana cikin mutanen Kirki .
2. Wasu kuma suka tafi akan kasancewarsa ba Salihin bawa ba , bashi da Aƙida mai kyau amma batun Lahirarsa yana ga Allah Ta'ala, akasin kashi na farko .
3. Wasu kuma suka tsaya (Tawaqqufi) tare da maida ilmin sha'anin Mukhtar ga Ahlinsa basu ɗauki banagare ba suna tsaka-tsaki , kamar su Shehunmu Al-Allamatul Majlisiy (Rahimahullah) a cikin "Bihar" bayan yayi dogon bayani tare da kawo Ruwayoyi a karshe ya zaɓi wannan ra'ayi na uku , kuma ya sanya Mukhtar a ƙarƙashin faɗin Allah :
وَآخَرُونَ اعْتَرَفُوا بِذُنُوبِهِمْ خَلَطُوا عَمَلًا صَالِحًا وَآخَرَ سَيِّئًا عَسَى اللَّهُ أَن يَتُوبَ عَلَيْهِمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ"
Ya ƙara da cewa : Don haka Ni game da sha'anin Al-mukhtar ina cikin waɗanda suka tsaya ko da kuwa abinda yafi shahara a tsakanin Malamai shine kasancewarsa daga cikin mutanen kirki ababen a godewa .
Duba Biharul Anwar ( Juzu'i na 45 Shafi na 339) .
Batun gaskiya da ina kan wannan ra'ayi na uku (ra'ayin Shehunmu Al-Allamatul Majlisi) amma daga baya na sauya sheka zuwa ra'ayin farko da mafi yawan Malaman Shi'a suka zaɓa , cewa Al-mukhtar Assaƙafi yana daga cikin bayin Allah mutanen kirki da suka taimaki sha'anin Ahlul Baiti (a.s) , bisa wasu dalilai da alamu da na fahimta daga ciki :
1. Ruwayoyin da suke sukarsa da nuna shi a matsayin maƙarayaci mai da'awar Annabta daga Littattafan Ahlussunna Wal jama'a suke , kuma akwai ƙamshin Umayyanci a cikinsu .
2. Na fahimci yadda gaggan Nasibawa irinsu Ibnu Taimiyya suke ƙinsa har suke kiransa da Mukhtar Alkazzab , lallai akwai alamar tambaya akan haka , ba haka kawai irinsu Ibnu Taimiyya suke ƙin mutum Irin Mukhtar ba , sha'aninsu ne yin sharri ga duk wanda sukaga ya rungumi lamarin Ahlul baiti (a.s) .
3. Irin gagarumin aiki da sadaukarwa da yayi ga sha'anin Alhlul Baiti (a.s) maƙiya Ahlul Baiti ba za su bar tarihinsa da farin fenti ba dole sai sunyi ƙoƙarin ɓatashi , da wasu dalilsi da na dogara dasu yasa nake tare da ra'ayin lallai Mukhtar bawan Allah ne na gari da ya taimaki Ahlul baiti (a.s) , zai ui yayi kuskure anan da can kuma dama shi ba Ma'asumi bane .
Tabbas ya ishi Al-Mukhtarus Saƙafi alfahari yadda Allah ya dinga ɗanɗanawa makasan Imam Hussain (a.s) azaba tun a Duniya a hannunsa , babu shakka ya sanyaya zuƙatan Ahlul Baiti da mabiyansu , shi yasa sharifai basu ƙara yin farin ciki , murna da ado ba tun bayan kashe Imam Hussain (a.s) sai da Allah ya tashi Al-Mukhtarus Saƙafi (Rahimahullah) , kamar yanda yazo a wata Riwaya .
Amincin Allah ya tabbata a gareka ya Mukhtar , ranar da aka haife ka da ranar da ka yi Shahada da ranar da za a tashe ka marabauci .
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
https://t.me/tafarkintsiratv
14/Ramadan/1444H - 5/4/2023 Miladiyya
0 Comments