– Kakakin gwamnatin kasar Iran ya tunatar da gwamnatin sahyoniyawan cewa ayyukan ta’addancin da take yi ba za su ci gaba da wanzuwa ba, a baya bayan nan ne dai wasu jami’an Iran biyu suka yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai a kusa da babban birnin kasar Syria.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, Ali Bahadori Jahromi ya ce ana amfani da gwamnatin Tel Aviv wajen aiwatar da ayyukan ta'addanci a wani yunkuri na kawar da jama'a daga fuskantar matsalolinsu na cikin gida.
"Gwamnatin yahudawan sahyoniya da sauran 'yan ta'adda na da dabi'ar aiwatar da ayyukan ta'addanci a kasashen waje a cikin mawuyacin lokacin da ake ciki, domin kawar da hankalin jama'a, kada a bari su bayyana matsalolinsu na cikin gida."
"Ayyukan ta'addanci dakukayi mana ba za su tafi ba tare maida martani ba," in ji kakakin, Press TV ta ruwaito.
Wasu mashawartan sojoji biyu na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) Milad Heidari da Meqdad Mahqani sun yi shahada a hare-haren sama da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai a ranar Juma'a a yankunan da ke wajen birnin Damascus.
0 Comments