Bismihita'ala.
Allahumma salli, ala Muhammadin wa ali Muhammad wa ajjil farjahum.
Shin dan uwa ko kasan wanene mukhtarus saqafi?
Sunansa: Mukhtar bn Abi-Ubaidata, Bn Mas'ud, Bn Amr, Bn Umair, Bn Auf, Bn Afarata Bn Umaira, Bn Saqif Ath-Thaqafi.
An haifi Mukhtar ne a Da'ifa, shekara ta 1 bayan hijirar Manzon Allah (saww), shi yasa ma ake kiranshi da Ath-thaqafi, wato mutumin Da'ifa. Larabawa suna kiran duk wanda aka haifa a Da'ifa da Ath-thaqafi.
Baban mukhtar Sahabi ne, yayi imani da Manzon Allah (saww), daga baya kuma a lokacin khalifancin Umar bn Khaddab ya baro garinsu ya dawo Madina tare da iyalansa, kuma yayi shahada ne a lokacin Umar din a yakin da musulmi suka ci kasar Farisa a lokacin Mukhtar na da shekaru 13 a duniya. Haka Mukhtar ya cigaba da rayuwa a Madina yana mai goyon bayan Imamu Ali (a.s), kuma yana cikin masu nuna son su da wilayarsu ga Imamu Ali (a.s) a sarari. Mukhtar jarumi ne mai tsananin jarumta, ya taimaki Imamu Ali (a.s) da duk iya karfinsa, kuma yana daga cikin wadanda suka yi wa Imamu Hasan (a.s) bai'a bayan shahadar Imamu Ali (a.s).
Mukhtar shine ya fara saukar da Muslim bn Aqil dan sakon Imamu Husain (as) a gidansa dake Kufa. Daga bisani dai Ubaidullahi(L.A) yasa aka kamo Mukhtar ya dake shi da sanda a idonsa! har Idon ya kumbura ya rufe, sannan yasa aka kai shi kurkuku, a can ya zauna har bayan shahadar Imamu Husain (a.s).
Bayan shahadar Imamu Husain (as) ne aka saki Mukhtar, bayan da Abdullahi bn Umar Muftin wannan lokacin kuma mijin 'yar uwar Mukhtar, ya nemi alfarma wajen Yazidu(L.A) kan a saki Mukhtar, sai Yazidu(L.A) ya aikawa Ubaidullahi da takarda kan ya saki Mukhtar din.
Ubaidullahi ya sake shi a bisa dole ba yanda ya iya, domin ya san sakin Mukhtar zai zame musa babbar barazana ga rayuwarsu.
Haka ya sake shi amma yace da shi ya kwashe kayansa ya bar Kufa a cikin kwana uku, idan ba haka ba kuwa zai sare wuyansa.
Hakan ta sa Mukhtar ya bar Kufa ya koma Hijaz da zama, yana ta alwashi ga Allah kan idan ya samu dama sai ya kashe duk wanda ke da hannu a kisan da aka yi wa Imamu Husain (as) da iyalansa a Karbala.
A shekara ta 66 bayan Hijra kuwa Mukhtar ya assasa rundunoni da iznin Muhammad Bn Hanafiyya dan uwan Imamu Husain, suka dinga tattaro mutane daban-daban masu goyon bayan daukar fansar jinin Imamu Husain (as). Haka suka shiga Kufa suka tunkude gwamnan Kufa na wannan lokacin, wato Abdullahi bn Mudi'u, ya zama yanzu Mukhtar ne gwamnan Kufa, haka kuwa yayi ta hada rundunoni domin kashe duk wanda aka san yayi musharaka a kashe Imamu Husain (as).
Haka aka shiga farautarsu a kowanne saqo da lungu na cikin garin Kufa da kauyukan dake zagayenta. Cikin manya-manyan yan ta'addan da Mukhtar ya kashe akawai:
UMAR BN SA'AD
SHIMR BN ZIL JAUSHAN
HARMALA BN KAHIL AL-ASADI. (Shine ya harbi jaririn Imamu Husain as)
UBAIDULLAHI BN ZIYAD (L.A)
SANNAN BN ANAS (L. A)
KHAULI AL-ASBAHI (L. A)
HUSAIN BN NUMAIR, da sauran tsinannun da suka taka mummunar rawa a wajen kashe Imamu Husain (as).
Ya zo a ruwaya cewa: A lokacin da aka zo wa Imamu Zainil abidina (as) da kan Ubaidullahi bn Ziyad da kuma Kan Umar bn Sa'ad, sai Imam (as) ya fadi yana Sujada yana cewa: "Na godewa Allah da ya nuna min ganin wannan daukar fansar kan Maqiyana, Allah kuma ya sakawa Mukhtar da alkhairi"
Mukhtar ya yi Shahada ne a hannun wasu masu bore ta bangaren mulkin Abdullahi Bn Zubair, suka kashe shi ta hanyar yi masa yankan rago!, suka rataye kansa a masallaci. Wannan ya faru ne ta dalilin tabar da shi da mutanen Kufa suka yi, suka ki dakewa a fagen fama suka sallama Mukhtar a hannun makiyan da Mus'ab bn Zubair dan uwan Abdullahi bn Zubair ya jagoranta.
Makashin Mukhtar wato Mus'ab Bn Zaubair bai tsaya nan ba, sai da ya kashe Matar Mukhtar mai suna Amratu bnt Nu'uman bn Bashir. Amratu matar Mukhtar mumina ce dakakkiya, domin kuwa Mus'ab ya bukaci da tayi bara'a ga mijinta Mukhtar, sai ta ce da Mus'ab: ta yaya zan yi bara'a kuwa ga mutumin da yake wuni azumi ya kwana sallah da daddare, kuma ya dauki alkawarin Allah da Manzonsa kan sai ya dauki fansar dan Manzon Allah?
Sai Mus'ab yace da ita: Ai kuwa sai na riskantar dake da mijinki. Sai ta ce da shi: Bayan wannan mutuwar ai aljanna ce!, ina rantsuwa da Allah ba zan taba rinjayar da son wani abu ba a birbishin son da nake yi wa Ali bn Abi Dalib (as)!. tana fadar haka sojojin Mus'ab bn Zubai suka kama ta suka fille wuyanta kuma suka qona kanta! Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'uun.
Ya zo a cikin littafin tarikhud-dabari juzu'i na 4 Shafi na 574, da kuma littafin Mawaqifus-Shi'a Juzu'i na 2 Shafi na 206 cewa itace Mumina ta farko da aka kasheta saboda son ta ga Ali Bn Abi Dalib (as)
Amincin Allah ya kara tabbata ga Mukhtar (r.a) da duk wadanda suka dafa masa babu ja da baya wajen daukar fansa akan Makasan Imamu Husain (a.s).
A irin wannan rana ce ta 14 ga watan Ramadan na Shekara ta 67, Mukhtaruth-Thaqafi yayi shahada yana da shekaru 67 a duniya. Kabarinsa na nan a cikin Masallacin Kufa, a gefen makwancin Muslim bn Aqil (as).
Amincin Allah ya tabbata agareka ranar da aka haife ka,ranar da aka kashe ka,ranar da za'a tashe ka kana mazlumi.
Allahumma ajjil liwaliyyikal faraj
14/9/1444
5/4/2023
By Muhammad Khalid
0 Comments