Da farko ina miqa saqon ta'aziya ta zuwa ga Allah (S) da kuma Manzon Allah (s.a.w.w.) da sayyida Zahra(As) da Imam Ali (As) da dukanin imamai har zuwa kan qa'im Al-muntazar da Sayyid (H) da daukacin Al'ummar musulmi juyayin rashin Nana Khadijah Matar Manzon Allah (s .a.w.w.).
Yau muna goma ga watan Ramadan, ranar da yayi daidai da wafatin sayyida Khadijah Al_kubra, Mahaifiyar sayyida Zahra (As).
Takaitaccen tarihin wafatin Nana Khadijah Matar Manzon Allah (S.a.w.w.).
Ummul muninana Nana Khadijah b'nt khuwailid, matar ma'aiki (S) tayi wafati ne ranar goma ga watan Ramadan shekara ta goma
Da aiko ma'aiki (S) wato shekara ta uku kenan kafin
Hijira, a lokacin kuwa tana da shekaru (65) a duniya.
Kafin wafatin ta dai Khadijah ta bada gudunmawa mai girman gaske wajen kare ma'aiki (S).
Da kuma cigaban tarda Musulunci a lokacin da yake cikin mayuyacin hali.
Saboda irin wannan gudunmawa da Nana Khadijah ta bayar ne aka
Ruwaito cewa: Manzon Allah (S) yana cewa:_
Badan kariya ta Abu Dalib ba (As) da kuma dukiyar Khadijah da kuma takobin Ali (As) da wannan Addinin bai tsaya ba da kafar sa ba.
Wannan wafati na sayyida Khadijah dai ya kasance babban Rashi ga ma'aikin Allah (S) da kuma "yarsa Fatima (As).
Yaxo cikin ruwaya cewa Sayyida zahra taxo gaban manzon (S) tana kuka tace : ina mahaifiyata , nana take sai mala'ika jibreel (As) ya sauko yace wa Annabi (S)
"Kace ma Fatima cewa Allah (T) ya gina wa mahaifiyar ta gida a Aljanna da zinare ".
Hakan kuma saboda da irin wannan babban musiba data sami ma'aiki (S) na Rashin wannan baiwar Allah kuma mujahida da kuma wafatin Baffansa Abu Dalib (S) kuma mai kare shi ya kira wannan shekarar da suna (Shekarar Baqin ciki).
Wacece Khadijah a takaice?
Itace Khadijah b'nt khuwailid bn Asad bn Abdul Uzza bn Qusay, tana daga cikin manyan matan Quraishawa kana kuma wacce tafisu kyau da Kyawawan halaye, tun kafin xuwar musulunci suna kiranta da suna "At Tahira" ma'ana (tsarkakakkiya) saboda irin kyawawan dabi'un ta , kuma ana kiranta da "Shugabar matayen Quraishawa".
Matsayin ta A gurin Allah kuwa wannan mai girma ne .
Saboda Allah (T) da kansa yake aiko mata da saqon gaisuwa .
Yaxo a cikin ruwaya : watarana Manzo Allah (S) yana zaune sai ga mala'ika jibreel ( As) yaxo yace mai :- ya ma'aiki ga Khadijah nan da qwarya in taxo kace Allah (T) yana gaishe ta nima ina gaishe ta, kace mata Allah (T) yace kayi mata bushara da cewa ya gina mata gida a Aljanna da zinare.
Allahumma sali Ala Muhammad wa'li Muhammad.
Shiyasa Allah (T) yake cewa :- mafi daukakar matayen Aljanna sune : Khadijah b'nt khuwailid, Fatima b'nt Muhammad, Maryama b'nt Imrana da kuma Asiya b'nt muxahim (matar fir'auna).
Amincin Allah (T) a gareki ya wacce Allah (T) yake sonki ya kuma yi miki Alqawarin dawwama a gidan Aljanna.
Amincin Allah (T) gareki ya farin cikin ma'aikin Allah (S).
Amincin Allah (T) gareki ya mahaifiyar Sayyida Zahra kuma sirika ga Zakin Allah (T).
Amincin Allah (T) ya cigaba da tabbata a gareki tun daga Ranar haihuwar ki har zuwa Ranar Alqiyama.
Assalamu Alaiki ya Sayyida Khadijah b'nt khuwailid.
Allah (S.w.t.) yasamu a cikin ceton ki Ranar mahshar.
Wassalamu Alaikum wa Rahma tullahi Ta'ala wa Bara katuhu🙏.
FREEDOM FIGHTERS NG.
0 Comments