TINQAHON DUNIYA DA HARKA ISLAMIYYAH(01)

 

Da za'a Tambayemu a ce, su waye Makiya Harkar Musulunci Lamba ta Daya?


Amsa itace Tinqahon Duniya.


A kula da kyau, Dinkahon Duniya(Global Hegemony)


muka ce, ba Kasar Amurika ko Ingila ko Haramtacciyar Kasar Sahayuniyyah kai Tsaye ba.


Tinkahon Duniya wata Gamayyar Matsiyata ne, Matsafa, Mashaya Jini, Makwadaita, Lalatattu, wadanda musamman tun bayan Rushewar Yarjejenjyar Warsaw da Rugujewar Tarayyar Soviet, a farkon Tis'inoni, suke kokarin shimfida ikonsu, da yada manufofinsu a cikin kasashen Duniya, ta hanyar tsarin Unipolar System, inda suka bawa kasar Amurika Karfi mara Misali, domin cimma manufarsu.


 Ba taron gamayyar 'Yan Tasha ne kawai ba, tsararrar Tafiya ce, mai ideology zaunanne da manufa da plan din cimma manufar tsararre. Kuma a wajensu wannan ideology din shi kadai ne hanyar tseratr da Duniya daga Hadari. Kuma sun yi Imani da hakan.


Mafi yawan Jagororin wannan tawaga ta shedan suna zaune ne a Kasar Amurika, Ingila da Haramtacviyar kasar Sahayuniya. Shi yasa wani Lokacin ake cewa wadannan kasashen, su ne Tinkahon Duniya. Amma gaskiyar magana shine, hatta Mutanen wadannan Kasashen suma suna Dandana Radadin da sauran Mutanen Duniya ke Dandanawa daga hannun Tinkahon Duniya. Sune ma victims din farko, sannan sauran mutane. Kai wani lokacin hatta Gwamnatocin wadannan kasashe, idan ka cire Haramtacciyar kasar Sahayuniya, suma suna shan tasu Azabar a hannunsu, idan akayi rashin sa'a ba nasu ne ke mulki ba.


Death to Amerika dinda muke fada, bafa da mutanen kasar Amurika muke ba, ba su muke tsinewa ba, kuna su ba Abokan Gabbarmu bane, suma victims ne da muke masu fatar wata rana su samu 'Yancinsu, ko kuma mu kwato masu, bayan mun samu namu.


Da Tinkahon Duniya muke, ideology dinsa muke tsinewa, shine death to Amerika, ba mutanen Amerika ba. Illa dai shi wannan Tinqahon zaune  yake zaune a cikin bangarorin gwamnatin Amurika ya rike mata wuya, ya hanata numfashi. Ya dorata saman Ideology (Nazariyyah) zaunanne, kuma da ita ne yake kokarin mamayar  Duniya. Shi yasa muke kai mata duka, domin sun riga sun cure, sun cakuda da juna, rabasu ba zai yiwu ba.


Wato abunda Tinkahon Duniya ya fara yi shine samun wajen zama, kafin ya fara kai raraka. Inda ya mamaye Turai ta Yamma, hade da kasar Amurika, a matsayin nan ne cibiyarsa ta yada manufofinsa zuwa sassan Duniya.


Turawan Yamma, da Mutanen kasar Amurika da Bakaken da aka kwasa aka kai can, domin Bauta, su ne Gamayya ta farko da Tinkahon Duniya ya fara Lakumewa. Har ta kai yanzu ya anshe masu duk wani bangare na rayuwa, sun fada cikin Mamaya wadda batada misali.


Yadda sauran kasashe suke abun Tausayi, su ma mutanen Turai da Amurika abun Tausayi ne, wani lokacinma sun fi kowa bukatar a tausaya masu, domin su ne wutar Bala'in wannan tsarin ke fara shafa.


Tinkahon Duniya ba Illuminati ko fremason kawai bane, su wani sashe ne nashi. Abun ya wuce nan da nisa mai yawa.


A rubutu na gaba za mu yi maganar yadda su ke mamayar Duniya da kuma Matsalarsu da Harka Islamiyyah.


Shamsudeen Hassan 

24/4/2023

Post a Comment

0 Comments