- Wani Bafalasdine ya kai wani gagarumin farmaki a ranar Talata a kudancin ‘Tel Aviv’, wanda ya yi sanadin jikkatar wasu sojojin mamaya biyu.
Bafalasdinen ya isa wurin taron sojojin mamaya a kudancin ‘Tel Aviv’, inda ya daba wa biyu daga cikinsu wuka kafin su kama shi, kamar yadda kafafen yada labaran Falasdinu suka rawaito.
Bangarorin gwagwarmayar Falasdinawa sun tabbatar da cewa wannan farmakin na mayar da martani ne ga hare-haren da 'yan mamaya suka kai kan masu ibada a masallacin Al-Aqsa.
Bangarorin sun jaddada cewa, al'ummar Palastinu za su ci gaba da tinkarar 'yan mamayar, da kare kasarsu da kuma haraminsu, kuma ba za su amince da mamayar yahudawa al-Aqsa ba.
Rafah al-Allouni/ Shaza Qreima
0 Comments