Yajin aikin gama-gari a garuruwan Falasdinawa domin nuna adawa da laifukan mamayar da Isra'ila ke yi

 


A wata zanga-zangar nuna rashin amincewa da hukuncin kisa da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi wa Mohammad al-Osaibi a kusa da daya daga cikin kofofin masallacin Al-Aqsa, da kuma ci gaba da aikata laifukan da ake yi wa Falasdinawa, an gudanar da yajin aikin gama-gari a kasar. 


Kamfanin dillancin labaran Wafa ya bayyana cewa, kwamitin koli na bin diddigi a yankunan Falasdinawa da aka mamaye a shekara ta 1948 ya yi kira da a shiga yajin aikin da ya hada da bangaren ilimi da tattalin arziki.


Kwamitin ya yi kira da a shirya tsayuwa a dukkan garuruwan wadannan yankuna, domin yin watsi da laifuffukan mamaya, muggan manufofin da ayyukan nuna wariyar launin fata.


Ta jaddada cewa laifin da sojojin mamaya suka aikata ya zo ne a cikin tsarin ci gaba da hare-haren da sojojin HKI ke kaiwa Falasdinawa a Kudus da al-Aqsa.


Rafah al-Allouni/Ruaa al-Jazaeri ce ta hada wannan rahoto Mahadi Tukur Almizan ya fassara maku.

Post a Comment

0 Comments