Amurka ta rufe websites ɗin mataimakin Sayyid Hassan Nasrullah da na gidan TV ɗin Hizbullah.

 


A wani yunkuri na Amurka a kwanakin nan ta sanarda kwace iko da websites 13, wanda ya tayarda kura akan 'yancin tofa albarkacin baki.


Ma'aikatar sharia ta Amurka tayi ikirarin cewa Websites din wasu mutane ne da kungiyoyi ke amfani dasu wadanda an sanyamusu takunkumi.


Daya daga cikin websites din da aka rufen sun hada da na Mataimakin Sakataren Hizbullah Sheikh Na'im Qassem babban website din Kungiyar tallafin 'yan gwagwarmayar Musulunci, wanda ake amfani da shi gurin samarda kudade don amfanin Lebanon,sai kuma website din gidan Talabijin din Al-Manar na kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Hizbullah.


Kamar yanda rahoton kotu ya nuna Amurkar ta samu damar kwace manartv.net,manarnews.net, da kuma naimkassem.net.


Tun bayan kwace websites din duk wanda ya ziyarci shafukan zai samu sakon gaisuwa neh kamar haka "Wannan Shafin an kwaceshi" sai kuma tambarin FBI da Department of Commerce kawai ne zaka iya gani.


Dukda haka shafin moqawama.org ya kasance yana budewa ta hanyar amfani da moqawama.org.lb, dukda farmakin da aka kaiwa shafin daga Amurka.


Wannan matakin na Amurka ya Sanya shakku a zuciyoyin al'umma inda suka nuna cewa wannan tauye 'yancin ɗan adam neh na tofa albarkacin baki.


Yanzun haka dai matakin Amurka din ya haifar da cecce kuce a kafafen sadarwa inda mutane ke nuna damuwa akan take hakkin 'yan adam din da Amurkar keyi.

Post a Comment

0 Comments