AN NEMI A DAKATAR DA WANI FIM DA AKA SHIRYA DOMIN BATA MUSULUNCI A INDIA SAIDAI KUMA Kotun ƙolin India ta ƙi amincewa a dakatar da fim ɗin 'The Kerala Story'

 



Kotun Ƙolin India taƙi hana sakin fim ɗin nan mai suna 'The Kerala Story'.


Alƙalai da suka saurari ƙarar sun yanke wannan hukunci sakamakon ƙorafin da aka yi musu na cewa ba a tantance fim ɗin ba a hukumar tantance finafinai.


Alƙalan sun ce, " Ka yi tunani bisa ƙoƙarin jaruman, da masu shiryawa. Mai shirya fim ɗin babu shakka ya kashe manyan kuɗaɗe a lokacin haɗa shi. Yanzu kamata ya yi a bar kasuwa ta yanke hukunci." Ko ya cika sharuɗa ko aka sin haka.


Kotun ƙolin ta ƙi sauraren ƙorafin ta kuma umarce su da su tafi Babbar Kotun Karela su gabatar da kukansu.


Kotun ta ce tana taka tsantsan kan abubuwan da suka shafi haramta fitar da fina-finai, in ji Suchitra Mohanty wanda da alaƙa da BBC.


Abin da fim ɗin ya ƙunsa a cewarsu, an nuna yadda aka riƙa yaudarar dubban 'yan matan Kerala aka sauya musu addini aka aika su ƙasashen da ke da tsattsauran ra'ayin addinin Islama irin su Syria.


Waɗanda suka soki fim ɗin sun ce an zuba ƙarya fal cikinsa, kuma wata farfaganda ake so a yaɗa wadda ba ta gaskiya ba. Shi ya sa suke so a dakatar da shi.


Post a Comment

0 Comments