An daure hamshakin attajirin dan siyasar Najeriya, Ike Ekweremadu , da matarsa da kuma dillalinsu su a gidan yari bisa laifin safarar sassan jikin dan adam, bayan sun kai wani yaro Birtaniya daga Legas, domin ya bayar da kodarsa ga diyar sanatan.
Sanata Ike Ekweremadu mai shekaru 60 da matarsa Béatrice mai shekaru 56, sun bukaci kodar matashin ga ‘yarsu Sonia mai shekaru 25 da haihuwa, kamar yadda kotun Old Bailey ta ce.
A baya dai an yanke wa mutanen biyu da Dokta Obinna Obeta mai shekaru 50 hukuncin daurin rai da rai.
Ike Ekweremadu, wanda alkali ya bayyana a matsayin wanda ke wasa da rayuwar dan adam, an yanke masa hukuncin daurin shekaru tara da watanni takwas a gidan yari.
Kotun ta kuma yanke wa Dakta Obeta hukuncin daurin shekaru 10 bayan da alkali ya gano cewa ya kai hari ga matashin.
An daure mata sanatan wato, Beatrice Ekweremadu na tsawon shekaru hudu da watanni shida a gidan yari kasancewar bata da hannu dumu-dumu a cikin laifin.
0 Comments