- Mahadi Tukur Almizan
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran [IRG] sun kama wani jirgin ruwan dakon mai na kasashen waje a mashigin ruwan Hormuz.
Rundunar sojin ruwa ta dakarun kare Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun kama jirgin ruwan dakon mai na kasar waje, wanda bisa dukkan alamu ya karya ka'ida, a ranar Larabar da ta gabata ne dakarun sojin ruwa na IRG suka kama jirgin a mashigin ruwan Hormuz.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto rundunar sojin ruwan Amurka ta 5 na cewa jirgin ruwan dakon man fetur ne mai dauke da tutar Panama mai suna Niovi.
A makon da ya gabata ne dai sojojin ruwan kasar Iran suka kama wani jirgin ruwan dakon mai mai dauke da tutar tsibirin Marshall a cikin tekun Oman tare da nusar da shi zuwa gabar ruwan kasar Iran bayan da jirgin dakon man ya afkawa wani jirgin ruwa na kasar Iran tare da kokarin guduwa da shi wanda ya saba wa ka'idojin teku.
0 Comments