Girgizar kasa mai karfin awo 6.5 ta afku a tsakiyar kasar Japan, an samu raunuka babu mutuwa.

 


- Mahadi Tukur Almizan


Wata girgizar kasa mai karfin gaske ta afku a tsakiyar kasar Japan a yau Juma'a, inda kafafen yada labaran kasar suka bayar da rahoton cewa an samu raunuka da rugujewar gine-gine.


Girgizar kasa mai karfin awo 6.5 ta afku a tsakiyar yankin Ishikawa da misalin karfe 2.42 na rana (1.42pm agogon Singapore) tsawon kilomita 12, a cewar hukumar hasashen yanayi ta Japan.


An dakatar da jiragen kasa na Shinkansen a tsakanin Nagano da Kanazawa, sanannen wurin yawon bude ido, amma ya koma aiki kasa da sa'o'i biyu, a cewar ma'aikatar hanyar jirgin kasa ta Japan.


Ba a bayar da gargadin yuwuwar faruwar tsunami ba.


Babban sakataren majalisar ministocin kasar Hirokazu Matsuno ya shaidawa wani taron manema labarai na gaggawa cewa, mutum daya ya kamu da ciwon zuciya bayan girgizar kasar, amma bai bayar da karin bayani ba.


Matsuno ya kara da cewa, ba a sami wata matsala ba a tashar makamashin nukiliya ta Shika da ke yankin, ko kuma a cibiyar Kashiwazaki-Kariwa da ke lardin Niigata da ke makwabtaka da yankin.


Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, hukumomin kasar Japan sun sake duba ma'aunin girgizar kasar zuwa maki 6.5 daga matakin farko na 6.3, tare da gargadin afkuwar girgizar kasar.


Wani jami'in hukumar kula da yanayi ya ce "wata  girgizar kasa na iya afkuwa mai girman gaske, musamman nan da kwanaki uku masu zuwa."


Ya bukaci mazauna yankunan da girgizar kasar ta afku da su ci gaba da sa ido na kusan mako guda, idan aka samu ci gaba da faruwar girgizar kasa mai karfin 6 ko sama a ma'aunin kasar Japan, wanda ya kai 7.


Matsuno ya ce gwamnati ta kafa wata cibiyar daukar mataki ga girgizar kasar karkashin jagorancin Firayim Minista Fumio Kishida.



Girgizar kasa mai karfin awo 6.9 ta afku a wani kauyen masu kamun kifi da ke yankin Noto dake wannan yankin a shekarar 2007, inda ta raunata daruruwan mutane tare da lalata gine-gine sama da 200.


Yankin Noto yanki ne na karkara a gabar Tekun Japan. Yawan al'ummar yankin na kusan 340,000, bisa ga kididdigar shekarar 2015.


Kasar Japan dai na cikin bala'in tunawa da wata girgizar kasa mai karfin awo 9.0 da ta afku a arewa maso gabashin kasar a watan Maris din shekarar 2011, wanda ya haddasa bala'in tsunami da ya yi sanadin mutuwar mutane 18,500 ko kuma suka bata.


Tsunami na shekarar 2011 ta halaka na'urori masu sarrafa wutar lantarki guda uku a tashar nukiliyar Fukushima ta Japan, lamarin da ya haddasa bala'i mafi muni da ya afku, da kuma hatsarin nukiliya mafi muni tun bayan Chornobyl.

Post a Comment

0 Comments