HAIHUWAR IMAM ALIYU AR-RIDHA (AS)

بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وآل محمد

TAKAITACCEN TARIHIN IMAM ALI AR-RIDA(AS); DAYA DAGA CIKIN IMAMAN AHLUL-BAYT(AS) KUMA KHALIFA NA 8 A JERIN KHALIFOFI 12 DA ANNABI MUHAMMAD(SAW) YAYI WASIYA DA SU:

Nasabarsa ta bangare mahaifinsa: shine Ali Rida bn Musa bn Ja'afar bn Muhammad bn Ali bn Husain; dan uwan Imam Hasan; ƴaƴan Ali Amirul-Muminin(as) da Sayyidah Fatimah Az-Zahra(as), ƴar Annabi Muhammad(saw).

Al-kunyarsa: Abul Hasan, Abu Ali...

Lakabinsa: Arrida, Assabir, Arradiyyu, Alwafi, Alfadil....

Tarihin haihuwarsa: Akwai sabanin masana tarihi da hadisi akan fayyace ranar da aka haifi Imam Rida(as), wasu kan ce; an haife shi a ranar Alhamis ko Jumu'a, 11 Dhul-Hijja, Dhul-Qa'da ko Rabiul-awal, a shekara ta 148 H ko 153 H. 

Ruwaya mafi shahara 11-Dhul-Qa'da-148H

Tambarin zobensa: Masha Allah la Kuwwata illa bil-Lahi.

Tsawon rayuwarsa: shekara 55.

Sarakunan zamaninsa: Abu Ja'afar Al-mansur, Muhammad Al-Mahadi, Musa Al-Hadi, Harunar-Rashid, Al-amin da Al-ma'amun; dukkaninsu sarakunan Abbasiyawa ne.

Tarihin shahadarsa: akwai sabani akan fayyace ranar da yayi Shahada, wasu masana kan ce yayi Shahada a ranar Jumu'a ko Litinin karshen watan Safar, inda ya yi shahada: Garin Duss a Khurasan (Iran).

Dalilin shahadarsa: Shayar da shi guba a lokacin khalifa Al-ma'amun.

Inda aka binne shi: Alkaryar San'abad a Duss Khurasan. A yau wurin yana cikin birnin Mash'had (Iran).

Bayan shekaru 16 da haihuwar Imam Arrida(as); daular Umawiyawa ta fadi, sai aka kafa Daular Abbasiyawa, wancan lokaci ya kasance lokacin da soyayyar Ahlulbayt(as) ta bunkasa; bayan da Al'umma ta fahimci matsayin su a wajen Allah(swt) da kuma kakansu(saw).

A lokacin, Soyayyar Ahlul-bayt(as) da Abassiyawa na tafiya kafaɗa da kafaɗa, saboda Al'umma ta fahimci irin zaluncin da banu Umayya suka yi musu, su kuma Abassiyawa saboda sun kifar da Azzalumar daular Banu Umayya, kamar yadda mahawarar Imam Kazim(as) da Haruna Al-abbasi ta shaida hakan; yayin da Haruna Al-abbasi ya ce; "Imam Kazim(as) kai ne wanda Al'umma ke yiwa mubaya'a cikin Sirri", sai Imam Kazim(as) ya amsa masa da cewa: "Ni shugaban zukata ne; kai kuma shugaban gangar jiki ne", ma'ana ni shugaba ne da Al'umma suka amince da ni a cikin zukatansu, kai kuma shugaba ne da Al'umma suka amince da kai a zahiri saboda tsoron salwanta rayukansu.

Hakika Allah(swt) ya horewa Imam Rida(as) kyawawen dabi'u, ya yi masa ado da duk wani karamci da daukaka sannan ya sanya shi alama ga Al'ummar kakansa(saw), yana shiryar da Al'umma hakikanin Addinin.

Hakika halayen Imam Rida(as) wani bangare ne daga halayen Kakansa (shugaban kyawawen dabi'u(saw) wanda kuma ya yi wa sauren Annabawa(as) fintinkau wajen cikar kamala.
Yayin da yake bayyana halayen Imam Rida(as), Ibrahim bin Abas ya ce; ban taɓa gani kuma ban taba ji ba, mutumin da ya fi Abil Hasan Rida(as) falala ba, domin shi bai taɓa aibata ko kuma cin zarfin wani ba, bai taɓa yanke maganar wani yayin da yake magana ba, bai taɓa kin biyan bukatar wani ba yayin da ya gabatar da bukatarsa, bai taɓa mike kafafuwansa a gurin zamansa ba, ko kuma zagin wanda yake karkashin ikonsa ko mabiyinsa ba, ya kasance mai barci kadan a cikin dare, dadai sauran siffofi na kamala da Imam ya keɓanta dasu.

Daga cikin kyawawen Dabi'unsa a yayin da yake shugabancin Al'umma: bai cika sanya mabiyansa aiki ba, idan ya nada wata bukata, shi da kansa ya kan tashi ya aiwatar da bukatarsa, kuma a yayin da ya bukaci zama da farko ya kan zamnar da wadanda suke yi masa hidima da farko kamar su mai gadi da sauransu domin ya basu darasi na cewa babu wani babbanci tsakanin Mutane.

Wannan kaɗan daga tarihin rayuwar Imam kenan, wanda taza wani abu ne da mutane zasuyi koyi da ita, domin samun tsira da kamala a cikin wannan duniya da kuma lahira.
وصلى الله على محمد وآل محمد.

Post a Comment

0 Comments