A ranar 14 ga watan Mayu, yayin nuna goyon baya ga falasdinawa, Muhammad Ali Alhouthi,daya daga jikin jigogin gomnatin siyasar Sana'a ya zargi saudiyyar da Jan kafa gurin cika alkawarin da ta dauka na daina yakar Yeman da kuma janye shingayen da ta sakawa Yemen.
Houthi ya nemi al'ummar kasar Yemen da su kasance masu hakuri da kuma kasancewa a cikin shirin ko ta kwana saboda kawancen na saudiyya tana Jan kafa musamman gurin dauke kawanyar da akayiwa kasar.
Dukda cewa Saudiyya ta halarci zaman sasancin da akayi a Oman tareda kungiyar gwagwarmayar Ansarullah kuma akasamu cigaba a tattaunawar har ta kaiga musayar fursunoni, da kuma yarjejeniya akan dauke toshewa hanyoyin Hodeida Port da kuma babban filin jirgin Sana'a International Airport, Amurka da Dubai sune kan gaba gurin ruguza wannan zaman tattaunawar.
Yunkurin Saudiyya na dakatar da yakin yana samun cikas,haka kuma kawancen na saudiya ya cigaba da zama barazana ga shirin zaman lafiya, inda aka cigaba da kai hare hare a iyakar Yemen din da yankin Saada da sauran wasu wurare.
Dukda haka Ansarullah ta cigaba da kariyar yankin Taiz.
Lokacin tattakin,Houthi ta kawo samun matsalar Na'urar kariyar Mizayil din Israila da ta samu lokacin da ake kai hare hare a guraren da ta mamaye,inda sukace Saudiya da UAE sun zubarda kimar su a idon Yemen haka kuma sunyi tambayar taya zasu kare kasashen da suka maida hulda da HKI.
Ansarallah ta nanata cewa muddin yunkurin samarda zaman lafiyar ya samu cikas tabbas zasu yi fito na fito da dukkan kasanshen kawancen saudiyyar tareda kai hare hare a Saudiyya da kuma UAE da makami mai linzami.
Houthi kuma ta kara jaddada goyon bayanta ga al'ummar Falastin da 'yan gwagwarmayasu,kuma sun bayyana cewa a shirye suke su tunkari Isra'ila.
'Yan gwagwarmayar ansan cewa sun mallaki makamai masu linzami wanda ke cin dogon zangon da zai iya riskar Isra'ila, hadi da makamin Zukfikar wanda anyi amfani da shi wurin kai farmaki a saudiyya a kwanakin baya.
Mutanen Yemen da Houthi sunsha alwashin taimakawa Falastinawa kuma zasu sanya hannu adukkan al'amarinsu kai tsaye don gwagwarmayarsu ta samu nasara.
0 Comments