'Yan gwagwarmayar Falastinawa sun harba makami mai linzami cikin garin Telaviv, don mayarda martani akan harin da Isra'ila ta kai a Gaza a ranar 10 ga watan Mayu.
Wata jaridar Isra'ila ta bayyana cewa mutum 6 neh suka samu raunuka bayan tashin wutar makaman masu linzami.
Telaviv, Asakalon, Ashdod, Sederot da sauran wasu anguwanni hadi da zirin Gaza makaman masu linzamin sun sauka a wannan yankuna.
A wani Bidiyo ya nuna yanda 'yan Isra'ila din keh tserewa suna neman mafaka biyo bayan saukar makaman masu linzami.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun bayyana cewa fiyeda makamai masu linzami 300 neh aka harba a cikin Telaviv da sauran wuraren da aka mamayen.
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta nuna matukar damuwarta akan harin da aka kai a zirin Gaza, inda suka tabbatar da cewa zasu cigaba da daukar fansar jinannen Falastinawa da ake shekarwa, sun kara da cewa jinanen Falastinawa bah abun wasa baneh kuma shine Jan layi na makurar hakurin mu.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa wannan aikin da suka fara na mamayar mai suna "Shield and arrow" zai cigaba da gudana neh babu gudu babu ja da baya a cikin wannan yanayi da suke.
0 Comments