MAKIYAN WAJE NE KE KOKARIN HADA FADA TSAKANIN FULANI DA HAUSAWA

 



Nace to ko da ganin wannan na san yin makiya ne, don dama tunda Turawan Ingilishi suka zo nan su sun dauka haka ne, su sun dauka dama mu kabilu ne, sun dauka da can akwai kabila sunanta Hausa, ita take mulki, sai Kabilar Fulani suka zo suka ci Hausa da yaki. Haka Mugal ya fada a ranar da ya ci Sakkwato da yaki, ya fada a ko 15 ga watan Maris ne, 1903. Yace, da can Fulani, sun ci kasar nan da yaki, saboda haka su suna da hakkin su mallaki kasar, amma mu yanzu Ingilishi mu kuma mun ci ku da yaki, saboda haka mu ne ke da hakkin mu mallake ku.


 To kaga su tun farko dama sun dauka akwai kabila sunanta Hausa, Fulani kuma suka zo suka ci ta da yaki. Don haka suke bayyana jihadin Shehu Usman Danfodiyo a matsayin yakin kabilanci ne. Saboda haka ko da aka fara wadannan maganganun, nace ok to mun san daga ina ya yo asali, ba daga wajenmu bane, daga wajen makiyanmu ne, don dama haka suke kallonmu. 


 Yanzu kuma (burinsu) a shuka gaba, ace ana fada tsakanin wannan da wancan, ana ta kashe-kashen da ba zai amfani kowa ba. Idan ka lura cewa kashe-kashen nan da ake ta ta yi tsakanin makiyaya da manoma, idan ka zauna ka tambayi wa yake amfana? Yana amfanar manoma ne ko yana amfanar makiyaya ne? Ina tambaya. Ba wanda ke amfana (a cikinsu). To, idan ka duba da kyau akwai wanda yake amfana wanda yake bukatar ya rage yawanku, ya hallaka ku, ya debi dukiyarku, ya mallake ku, ya maishe ku bayi, shi yake amfana da wannan, kuma shi ya kitsa.


 Don akwai sayayyun shafuffuka, masu maganganun nan ta shafuffuka (a internet) ai wasu sayayyu ne. Sai su yi ta zuba ashar, su yi ta zage-zage da jafa’i wai su Hausawa ne, suna zagin Fulani. Nake cewa aiko duk wanda zai yi wannan rigimar, kila tunda su Fulanin da suke kiwo ana gane su tunda suna tare da shanu ne, kila su kace su gasu nan suna da shanu ka je ka bi su ka shanun a kwashe a karkashe su, amma na gari ban san yadda za ka yi da su ba.


 Domin ni na san cikin garin Zariya, idan ka shiga cikin garin babu wani gidan da babu Bafullatani, sai dai idan ka zo kisan Fulani, to ina jin idan ka je wani gidan za ka ce wannan kan na Bafullatani ne, sai ka cire kan kabar gangan jikin na Bahaushe. Wani kuma za ka ga kila daga bangaren dama kana ganin Bafulatani ne, sai ka yage rabin ka wurgar ka bar daya ragowar. Tunda duk an caccakude ne an yi auratayya. 


Sai dai idan za ka daddatsa ne ka fitar da wadansu bangarorin jiki kace wadannan da ka tattaro na Hausawa ne, domin ba gidan ba za ka je ka sassara mutane ba. Ko dai ka cire kai ne ko wani abu, kila ka cire hannuwa da kafafu ka bar gundulmi, amma da yawa ma ina jin sai ka cire kan. Ko ba a lura ba? 


Wannan wani abu ne da ba zai yiwu ba sam-sam. To, fadan da ba hankali a cikinsa sam-sam, amma an jefa mu a ciki mun fada cikinsa. 


To kuma kashe-kashen da ake yi wanda ba ma shi da ma’ana sam. Ka rasa shi mai kisan ma bai san me yasa yake yi ba, shi wanda aken kashewa bai san me yasa ake kashe shi ba. Kisa ne kawai ake yi.



— Cibiyar Wallafa

www.cibiyarwallafa.org

Post a Comment

0 Comments