MU BA ZA MU DAINA ADDINI BA!

 



Mu dai abin da muke ce musu, kun gammu nan, yadda kuka gammu muna addinin nan to nan gani nan bari, mu ba za mu daina addini ba yadda kuka gammu muna yi. Idan kuma kun ce ku harbi ne, to shikenan ku ba da kokari, kowa ya yi nasa. Allah Ta’ala zai yi hukunci tsakaninmu da ku. Hukuncinsa kuma nan da nan ne. Amma ba dai ku tsammaci cewa wai za a bi ku ba, ko a fasa ba, ba fa za a fasa ba!


 Ballantana abin ma sai ka sha mamaki, don Allah mene ne a Quds? Kawai an fito ana goyon bayan wadanda ake zalunta, amma kai harbi za ka yi? To mu fa abin da suke mana, hatta ma daurin aure ma da jana’iza suna zuwa da bindiga ne wajen. Wani lokaci ana daurin aure sai gasu sun zo sun saka jajayen kyalle a kan bindigoginsu. Walima ana yi sai ka ga sun zo da bindiga wai a tashi. An raba abinci ma ana ci suka ce a tashi kawai, idan ba haka ba sai su bude wuta.


 Addu’a ma idan ana yi (ba a tsira ba), akwai wani lokaci da addu’a ce aka hadu ana yi a makabarta, suka ce a tashi kawai idan ba haka ba za mu bude wuta, don mu an umurcemu ne mu bude wuta kawai. Su an ce musu kawai su yi kisan kai ne, shikenan.


 Ko lokacin da za mu je Birnin Kebbi, sai muka bi ta Tsafe, lokacin sun saka wani ‘roadblock’ mai tsawon gaske da sai a yi awanni baka wuce wajen ba. To shikenan, kafin mu je sai aka yi magana da su aka ce gamu nan nine zan zo na wuce za mu je Birnin Kebbi ne. Sai suka ce to shikenan. To sun saka dogon layi ta dama, sai suka ce mu biyo ta hagu. Sai muka biyo ta hagu, suka buda mana, mu sai muka wuce. Dogon layi ta hagu da dama, idan ka fito Sakkwato dogon layi, ta nan idan ka fito ta Zariya shima dogon layi. To haka nan. Muka wuce dai.


 To can sai wasu ‘yan uwa suka zo daga baya a makare, kawai sai suka bi ta hagu din. Haba! Allah dai ya kiyaye da sun bude musu wuta. Suka ce ai mu mutanen Malam ne. Sai wani babbansu ya umurce su da su dakata. Yace musu ku daina yin haka nan, kun ga Malam ya zo nan ya wuce lafiya lau, saboda an yi mana magana ne, don ku sani mu an bamu umurni ne, ance har dabbobi mu harbe, kuma wadannan idan suka bi umurnin harbe ku gabadaya za su yi. Har dabba an ce su kashe ne. Ka kashe kowa da komai ma kenan, ba kowa da kowa ba, har dabba ma. Yace umurnin da aka bamu kenan.


 Ka ga irin wannan, tunda abin da suka sani kawai su za su yi harbi ne, to ya za ka yi da su? Sai dai idan ba za ka rayu ba, ka fasa rayuwa. Za ka fasa rayuwa ne? Shikenan, ya rage musu.


— Cibiyar Wallafa

Post a Comment

0 Comments