Musulmai a Kerala sunyi zanga zanga kan cin zarafin musulunci da kaka gidan da 'yan addinin Hindu ke yimusu a Indiya.

Dubban musulmi neh dai suka fito zanga zangar a kudancin Kerala ta Indiya,sun bi sahun zanga zangar neh don nuna adawa da nuna kin jinin musuluncin da ke kara yaduwa da kuma ta'addancin da 'yan addinin Hindu suke yimusu a tsaka da tasowar 'yan kaka gidan addinin Hindun.

Masu zanga zangar sun shiryata neh a Kerala Muslim Jama'at Federation (KMJF), inda suka hadu a gefen garin Kollam a ranar Assabar don tunawa da cikar kungiyar Federation din Shekara 40, sun nuna damuwa akan yanayin da musulmi suke a kasar.

Sunyi ta rera take da yake nuna adawa da Hindutva da yake karfafa 'yan kaka gidan da ke neman mayarda indiyar kasa ta 'yan addinin Hindu din kadai ba tareda wanzuwar addinai mabanbanta ba a kasar.

Tattakin ya maida hankaline akan wayarda kan al'umma kan karuwar cin zarafin musulunci da kuma illarsa ga al'ummar kasar.

A lokacin gabatarda taron wasu daga cikin mahalarta taron sun nuna kin amincewarsu da ma'aikatar National Registration of Citizens (NRC) da kuma Uniform Civil Code.

Haka kuma sunyi karin haske kan kazancewar lamarin inda ake farmakar duk wani taro na musulmi ciki harda masallatai a fadin Indiya.

Masu zanga zangar sun nemi baiwa musulmin kasar kariya da kuma kare 'yancinsu a matsayinsu na mafiya rinjaye a 'yan kadan din kasar,haka kuma sunyi kira da hadin kai ga musulmin kasar.

Tattakin ya tunatarda zanga zangar da aka gabatar a shekarar 2019 lokacin da musulmin Indiya suka nuna kin amincewa da tsarin ayyana NRC din a fadin Indiya.

Musulmin sun nuna damuwarsu kan cewa tsarin zai iya zama silar rasa 'yancinsu na zama 'yan kasar kuma za'a iya amfani da shi wurin nuna banbanci a tsakaninsu.

Haka kuma Hukumar Uniform Civil Code wata hukuma ce da aka ginata akan sanya dokokin da zasu shafi kowa a kasar ba tareda la'akari da addini ko jinsi ba, wanda ya jawo cecekuce da damuwa akan makomar wasu addinan a kasar.

Zanga zangar Kerala din ta zamo murya ceh ta dukkan musulmi dake adawa da kin jinin musulunci,'yan kaka gidan Hindu,da kuma banbancin da ake nunawa a bangaren shariar kasar, inda suka nemi a baiwa musulmin tsaro da 'yancinsu na zama 'yan kasar Indiyar.

Post a Comment

0 Comments