Rahoto ya nuna Hadaddiyar Daular Larabawa ta karbi Tallafin kayan yaki biyo bayan Farmakin da Yemen ta kai a Shekarar 2022



Kamar yanda littafin da aka rubuta mai suna "Trump's Peace" Wanda wani Dan jaridar Isra'ila ya rubuta mai suna Barack Ravid.

Tallafin yana zuwa neh biyo bayan farmakin da Ansarallah ta Yemen ta kai a UAE din ta hanyar amfani da jirgi maras matuki inda suka farmaki tsakiyar garin Abu Dhabi.

Littafin ya bayyana cewa Isra'ila ta wargaza wani komitin da ya hada da Jami'an Mossad da sojin UAE din, haka kuma sunyi jigilar baturora daga na'urar "Spyder Air Defence" don nuna goyon bayansu biyo bayan harin.

Tallafin da ya fito daga Telaviv ya kara jawo kakkausar suka daga Amurka wanda ya sanya takun saka tsakanin Abu Dhabi da Joe biden na Amurka.

UAE da Isra'ila sun mayarda alaka a tsakaninsu neh a shekarar 2020 tareda tallafawar Amurka, wanda yayi silar karfafa alakar kasuwanci da tsaro ga kasashen biyu.

UAE ta kasance mai goyon bayan Isra'ila ne a majalisar dinkin duniya ta hanyar hana sukar Isra'ila din akan abinda take yiwa falastinawa.

Bugu da kari UAE da Isra'ila suna kan shirin mamayar wani yanki na Yeman don samun damar bude wani sansanin soji na hadin gwiwa na sojin ruwa wanda akayi kiyasin jiragen ruwa fiyeda dubu ashirin zasu iya bi a wannan shekara.

Post a Comment

0 Comments