Kafin kayi Duka, kasan wanene Maƙiyinka tukunna. Da ace Buhari ko El-rufa'i ko Gauduje ne Asalin MAƘIYANMU, mu 'Yan Harka Islamiyyah, to da wata Ƙila Jefa Ƙuri'ah, irin wannan da ake yi a Najeriya ta Dan Amfanemu.
To amma mu mun fi kowa sanin dawa muke Kokawa. Mun fi kowa sanin Maƙiyinmu na Asali. Idan muka barshi, muka dawo Fada da Karen Karenshi, to mun ci baya, kuma zai mana kisan farat Ɗaya.
Tinƙahon Duniya, wanda ya Danƙar mana Tsarinsa na Danniya, yake kwashe mana Dukiya. Shine Warin karawarmu, kuma dashi muke Faɗa. Kuma dukar da muke tana kai masa, kuma yana jin zafi. Alhamdulillah.
Ta yiwu wani yace ta yaya kuka san Dukanku na kai masa? Sai mu ce ta hanyar Bannar da yake ci gaba da yi mana. Ta hanyar Kisa da Ɗauri da Rusau dinda yake mana ne. Ta nan muke gane yana dakuwa.
Duba da Kyau ka gani, za ka ga babu Banbanci Tsakanin Rusau ɗin El-rufa'i Dana Haramtacciyar Ƙasar Israel. Hatta kalar Yadda Jami'an Rusau ɗin ke fita tare da gamayyar Sojoji masu Kisa, duk kala Ɗaya ne. Wannan na nuna kenan tsarin kala guda ne. Kuma daga waje Ɗaya ya fito.
Ta yiwu wani yace to ku wane irin duka kuke masa? Sai mu ce Wayar da Kan Al-umma game da yanayin da suka jefamu na Bauta. Da farfado da Tarihinmu na kwarai, ta hanyar kira zuwa ga a komawa bin tsarin Allah. Wannan ne basa so. Domin shine kawai zai iya kawar dasu. Shi yasa suke kashemu kamar Farin Dango, ba Tausayi ba Jinƙai, suke rusa muhallanmu, suke ɗaure mu.
Wannan ne Dalilin hanawa Malaminmu passport. Sun fi son ciwo ya canyeshi, domin su huta dashi. Sai gashi Allah ya fito masu ta inda basa zato, ya taimaki bawan sa a inda basa Tsammani.
Masu ganin ta hanyar zaɓe ne kawai za su iya Ƙwatowa kansu 'Yanci, muna masu fatan Alkhairi. Kuma ya kamata su san cewa wata Ƙila mun banbanta da su wajen Tashkhisin Maƙiyinmu. Ta yiwu nasu Maƙiyin shiga zaɓe na iya maganinsa. Amma namu kam sai dai Muwajaha da Maƙawama.
Shawararmu garesu shine su bi a Hankali, kada su saka dukkan Aminci ga duk wani wanda basu ba, kada su yadda da duk wani wanda baya gani da kalar nasu idanun. Domin yana iya Juya baya, idan yaji matsin Lamba.
Ga sauran 'Yan Uwa kuma, mu sani hanyar kenan fah. Babu wata bayan wannan. Da akwai wata da Allah bai saukar da Suratul-Kafiriun ba. Da akwai wata, da Allah bai haɗa Yaƙin Badar ba. Da akwai wata da ba'a jiwa Ɗan gatan Allah Annabin Rahama ciwo a Ranar Uhud ba.
Da akwai wata da ba'a ƙona gidan Sayyada ba, da ba'a matseta a bayan kyaure har tayi Ɓari ba. Da akwai wata da ba'a Sari Imam Ali Hydar a Maɗiga ba, kuma da bai yi Jamal da Siffin da Nahrawan ba. Da akwai wata da ba'a sari Imam Hassan a cinya ba, kuma da bai cakawa Mu'awiya wuƙa a wuya ta hanyar Sulhu ba.
Da akiwa wata da ba'ayi waƙi'ar Karbalah ba, da ba'a shahadantarda Imamai ba.
Da akwai wata da Shehu Dan Fodiyo bai yi Jihadi ba, da Imam Khumaini bai yi Revolution ba.
Babu wata sai ita, kuma yanzu lokacin Sayyid Allamah ne. Shi ya tsaya kyam a kan Tafarki, bai sauya ba, bai gudu ba, bai fasa ba, bai sassauta ba.
To mu me muke jira.....??? Wane sassauci muke tsammani...???
Idan dai a kan turba muke, wadda kuma hakan ne, to dole duk Azabar da suka sha, muma sai mun sha irinta. Ai jiki bai fi jiki ba. Kuma duk cikarmu Al-jannah kala Daya muke nema.
Sabati dai ya Allah...
Shamsudeen Hassan
0 Comments