Ranar Litinin ministan cikin gidan saudiyyar ya sanarda yankewa 'yan Bahrain din hukunci sabida samun su da hannu a harkokin ta'addanci a gidan yari.
Ma'aikatar tana zargin matasan ne da safarar kwayoyi da kayan fashewa zuwa cikin kasar saudiyyar, haka zalika suna boye kayyayyakin a guraren da keda yashi daga baya su mikasu ga shugaban magarkamar tasu.
Bugu da kari ana zarginsu da samarda matsuguni ga wadanda ake nema ruwa a jallo daga Bahrain.
An yanke hukuncin kisan ne ga Jafar Sultan,Sadiq Sameer a kotun daukaka karar saudiya a watan Janairun 2022.
An kama Samir da Sultan ne a a ranar 8 ga watan Mayun 2015 a titin Sarki Fahad, haka kuma ana zarginsu da yunkurin fasa gadar da ta hada Bahrain din da Saudiyya.
Matasan dai sun musanta zargin da akeyimusun inda suka nunan cewa bita da kulli ne ake yimusu na siyasa.
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun nuna damuwa akan azabtarwar da ake yiwa matasan don su bayyana gaskiya lokacin da aka kamasu.
Biyo bayan wannan neh dai al'ummar kauyen Dar Kulaib dake cikin Bahrain suka gudanarda zanga zangar nuna kin amincewa da matakin da kasar saudiyyar ta dauka akan matasan guda biyu.
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da dama dai sun nuna damuwa akan lamarin inda suka bayyana cewa saudiyyar ta kara adadin mutanen da take yankewa hukuncin kisa daga shekarar 2020 zuwa shekarar 2022 wanda suka nuna saudiyyar bata tuntubar mutanen kasashen waje yayin yanke irin wannan hukuncin.
Bayan yanke hukuncin wata kungiyar Malaman addinin musulunci sun yi allawadai da matakin saudiyyar haka kuma sun mika ta'aziyyarsu zuwaga 'yanuwa da abokan matasan guda biyu da suka kira da "Shahidan Kasa guda Biyu".
0 Comments