SHAHADAR IMAM JA'AFAR AS-SADIQ (A.S)
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وآل محمد
قال الإمام الصادق (ع):- أحيوا أمرنا رحم الله من احيى أمرنا
Imam Ja'afar As-Sadiq (as) shine Imami na shida (6) acikin limaman shiriya su goma shabiyu (12).
Nasabarsa ta ɓangaren mahaifinsa
Muhammad (Bakir) bn Aliyu bn Hussaini Ɗa agun Sayyida Fadimatuz Zahra'u (s.a).
Mahaifiyarsa
Ummu Farwa bnt Qasim bn Muhammad bn Abubakar.
Laƙubbansa: Assadiq, Assabir, Alfadil, Aɗɗahir, Alkamil, Almunji.
Alkunyarsa: Abu Abdullah
An haifi Imam ranar 17 ga watan Rabi'u Auwal bayan hijira da shekara 83 a garin Madina, ya rayu a duniya na tsawon shekara 65, kuma yi Imamanci na tsayon shekaru 34.
Matar Imam Ja'afar (as) itace Fadimatu bnt Hussaini bn Ali bn Hussaini (as), Sauran kuma matan (Kuyangu) ne.
Yanada 'ya'ya kamar haka: Isma'il, Abdullahi, Musa, Ishaq, Muhammad, Abbas, Ali, Farwa, Asma'u, Fadimatu.
Imam yayi Shahada a ranar 25 ga watan Shauwal hijira ta 148H, Yayi Shahada a garin madina. An bizne shi a makabartar baqiyya a madina.
Imam yayi Rayuwa a lokacin siyasa mai tsananin gaske, wato siyasar Umayyawa da Abbasiyyawa, inda Imam a dai-dai wannan lokaci kuma yasamu dama na yaɗa fikira na Addinin babansa da karatuttuka na zamaninsa, wanda takaiga Imam yana da ɗalibai na kowane fanni a wancan lokaci, inda a yanda tarihi ya nuna cewa har shuwagabannin Mazhabobin da ake dasu yanzu duk ɗaliban Imam Ja'afar (as) ne.
A haka bayan Imam yasamu wannan dama ta yaɗa karatuttukan addini sukuma Umayyawa da Abbasiyyawa suna can suna faɗa akan mulki, wanda a karshe Abbasiyyawa sukayi nasara kan Umayyawa.
Bayan Abbasiyyawa sun karbi mulki sai hankalisu ya dawo kan gwagwarmayar Imam wanda itace fargaba gun Abbasiyyawa.
Imam Ja'afar an shahadantar dashi ta hanyar Guba, dalilin shine irin motsi da fito na fito ga azzalumai da yake na kin yarda da zalunci, sai suke gani cewa mulkin da suke takama dashi akwai barazana, kuma Imam yana samun goyon bayan mutane, akwai barazana sosai aciki mulkin su domin yafara samun tangarda, wannan ne yajawo suka ɗau matakin kawar da Imam Ja'afar Sadiq (as).
Saboda hakane MANSUR Mai mulki a lokacin, Yaga dole suyi wani abu dazasu kuɓutar da martabarsu da martabar mulkinsu sai suka ciyarda Imam ƴaƴan itatuwa masu guba wanda shine yazamo sanadiyyar shahadar imam Ja'afar (as). Imam yayi shahada ne a ranar 25 ga watan shawwal shekara ta 148 bayan hijira a lokacin Imam yana da shekaru 65.
Wannan kadan kenan daga cikin tarihin sa.
وصلى على محمد وآل محمد
0 Comments