Wata Sabuwa: Har yanzu Muna kokarin domin daidaita tsakanin "Isra'ila" da Saudiyya - Inji NSA na Amurka.


 


Mai ba Shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaron kasa, Jake Sullivan, zai je Saudiyya a karshen wannan makon don tattaunawa da shugabannin Saudiyya, ciki har da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman (MBS), da kuma jami'an Indiya da na Masarautar Daular Larabawa.  


Sullivan ya ce "A karshen mako zan je Saudiyya don ganawa da shugabanninsu."


Sullivan, wanda ke magana a ranar Alhamis a wata cibiyar bincike ta Washington, ya ce har yanzu Amurka tana kokarin daidaita dangantakar dake tsakanin Isra'ila da Saudiyya.


"A ƙarshe samun cikakkiyar daidaituwar al'amuran na su zai amfanar da Amurka. Mun bayyana hakan a fili," in ji shi.


Sullivan ya kara da cewa "Amatsayin alamar da ke nuna cewa da gaske muke dangane  da yadda muka mayar da hankali kan wannan al'amarin, ba zan kara cewa komai ba don kada in hargitsa kokarin da muke yi kan wannan batu."


Ziyarar Sullivan a yankin na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Washington da Riyadh ta yi tsami tun bayan ziyarar da shugaban Amurka ya kai masarauta a bazarar shekara ta 2022, duk da cewa kasashen biyu na ci gaba da yin aiki tare kan batutuwa da dama ciki har da na baya-bayan nan a Sudan.


Shugaban Amurka Joe Biden ya soki Riyadh kan kare hakkin dan Adam da manufofinta na makamashi, har ma ya yi kira da a yi nazari kan dangantakar da ke tsakaninta bayan matakin da masarautar ta dauka a watan Oktoban da ya gabata na rage yawan man da take hakowa. Sai dai Saudiyya na taka muhimmiyar rawa a yankin kuma ziyarar Sullivan wani bangare ne na muradin kusantar juna.


Sullivan ya ce "Takwarorina na Masarautar da Indiya za su zo Saudi Arabiya domin mu tattauna kan sabbin hanyoyin hadin gwiwa tsakanin New Delhi da Tekun Fasha, da kuma Amurka da sauran yankin." Ya ce halin da ake ciki a Yemen zai kasance wani muhimmin bangare na tattaunawar da za a yi a karshen mako.


Sullivan, ya kuma zurfafa magana kan batutuwan da suka shafi Gabas ta Tsakiya, tun daga Iran zuwa Syria da Iraki zuwa rikicin “Isra’ila” da Falasdinu. Ya kara da cewa: "Alkawarinmu na gabas ta tsakiya bai gushe ba." Ya kara tabbatar da cewa Washington za ta yi duk abin da zai hana Tehran samun makaman nukiliya.


Da aka tambaye shi Kan  lokacin da za a gayyato firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zuwa fadar White House, sai ya amsa da cewa: "Idan muna da nufin gayyata, zamu sanar da."

Post a Comment

0 Comments