Gwamnatin mulkin soja a Sudan, ta kai ƙarar wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya dan asalin ƙasar Jamus a bisa zargin rura watar rikicin da ke faruwa a ƙasar a maimakon sasanci, ta kai ƙarar ne wajen Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Gutteres.
Janar Abdel Fattah al-Burhan shugaban gwamnatin soji, ya zargi wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya dan asalin kasar Jamus, Volker Perthes da ƙara rura watar rikicin da kasar ke ciki.
Ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje, a Sudan ta bayyana Volker Perths a matsayin mutumin da suka cire fata daga samar da sasanci daga gareshi.
A cikin watan Afrilun da ya gabata ne dai sojojin kasar Sudan da kuma rundunar kar ta kwana ta RSF karkashin jagorancin tshohon mataimakin shugaban kasa Mohamad Hamdan Daglo suka fara kai wa juna hare-hare.
0 Comments