Amurka Na Ƙara Jibge Sojojin ta A ƙasar Syria.

 


Majiyoyin cikin gida sun bayyana cewa a ranar Laraba 7 ga wannan wata na Yuni anga ƙarin sojojin Amurka daga Iraqi zuwa haramtattun sansanonin Amurka da ke yankuna ƙasar Syria da a ke haƙar mai a yankin aljazira.


A na ganin wannan dai a matsayin ƙoƙarin ƙara gyara wurin zama domin horar da ƴan tawaye masu ƴaƙar gwamnati. 



Sojojin sun shigo ƙasar ta Syria ne ta bodar Al-Waleed wadda ke yankin da ƴan tawayen da Amurka ke mara wa baya ke iko. 


Wannan a yarin shine na biyu, kwanaki ƙaɗan kafin wannan wasu adadi su shigo ƙasar ta Syria, wanda a ƙalla mota 25 ne na sojojin suka shigo ta yankin Hasaka. 


Wadannan ƴan tawaye da Amurka ke mara wa baya dai ƙurdawa ne, Amurka ke basu Kuɗaɗe da horo irin na soji.

Post a Comment

0 Comments