Mutanen ƙasar Sudan sun samu damar fitowa domin yin sayayya a kasuwanni bayan da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki.
Wannan wata sabuwar yarjejeniya ce da Saudiyya da Amurka suka samar a ƙasar ta tsawon awa 24, yarjejeniyar ta fara aiki ne da misalin karfe 6 na safe agogon ƙasar.
Ana fatan dai wannan yarjejeniya ta wajen kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a ƙasar tun 15 ga watan Afrilun da ya gabata, tsakanin rundunar shugaban gwamnatin mulkin soja ta ƙasar Janar Abdel Fatah Alburhan da kwamandan rundunar sa kai ta RSF Hamdan Dagalo.
Wannan yarjejeniya ba ita ba ce ta farko, a baya an ƙulla wasu yarjejeniyoyin sai dai basu biya bukata ba.
0 Comments