Anyi garkuwa da manoma a Pandogari dake Jihar Neja.

 



Pandogari na ɗaya daga cikin garuruwan da aka kaima hari, wani mazaunin garin ya tabbatar ma manema labarai faruwar lamarin a garin na Pandogari inda aka yi  garkuwa da manoma. 


Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa an samu nasarar karbo wasu daga hannun ‘yan bindigar bayan an basu kudaden fansa, haka nan kuma akwai wasu mutanen da suka samu kubuta daga hannun maharan a lokacin da suke kokarin shigar da su daji.


A ranar Litinin ɗin da  ta gabata ne dai, gungun makasa suka afka wa yankin Allawa da ke karamar hukumar Shiroro, inda suka kashe mutum  guda, tare da sace shanu fiye da 100 da tsakar rana. 


Rahotonni sun nuna ce cewa baya ga tarin dabbobin, makasan da suka kai farmaki kan yankunan na Allawa da Pandogari, wadanda ke kananan hukumomin Shiroro da Rafi, sun yi awon gaba da manoma fiye da 55, a yayin da suke tsaka da aiki a gonakinsu, ciki kuma har da mata da ƙananan yara, yayin da saura suka ruga cikin daji, don tsira da rayukansu.

Post a Comment

0 Comments