Hukumomin Burkina Faso, sun yada da matakin makobciyar kasar Mali, na neman tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar cewa da Minusma ta san inda dare ya yi mata, ta fice daga kasar ba tare da wata-wata ba.
A cikin wata sanarwa, gwamnatin rikon kwarya ta Burkina Faso ta sanar da cewa ta lura kuma ta yi maraba da "hukuncin jajircewa" na hukumomin rikon kwarya na Mali na neman janyewar tawagar ta MINUSMA cikin gaggawa.
Hukumomin Burkina Faso sun kuma bukaci babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da ya kintsa shirye-shiryen janye sojojin Burkina Fason da ke Mali a cikin tawagar ta dakarun na MDD. Burkina Faso ita ce kasar da ta fi ba da gudunmawar soji ga tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya tun 2013 a makwabciyarta kuma shugaban rikon kwarya na yanzu Kyaftin Ibrahim Traore shi ma ya taba kasancewa cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Burkina Faso da aka tura a Mali, musamman a yankin Timbuktu.
A karshen makon da ya shude ne Hukumomin Mali, suka bukaci janyewar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar ba tare da wata wata ba.
0 Comments