Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya sanar a ranar Lahadi cewa, "dangantakar da ke tsakanin Beijing da Washington a halin yanzu ta kasance mafi muni tun daga shekarar 1979.
Gang ya shaidawa sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken cewa fayil din Taiwan na wakiltar "mafi girman barazana" ga dangantakar China da Amurka.
Gang ya kara da cewa, batun Taiwan shi ne jigon moriyar kasar Sin, kuma shi ne batu mafi muhimmanci a huldar dake tsakanin Sin da Amurka.
Kuma ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin ya amince ya kai ziyara a Washington, bayan ya yi "tattaunawa mai ma'ana" da takwaransa na Amurka, Anthony Blinken, a babban birnin kasar, Beijing.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matt Miller ya ce Blinken ya mika goron gayyata ga takwaransa na kasar Sin kuma sun amince da sanya ranar ziyarar a daidai lokacin da bangarorin biyu suka ga ya dace.
Kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua ya bayar da rahoton cewa, Blinken wanda shi ne wakilin farko na Amurka a matakin minista tun bayan da gwamnatin Biden ta karbi mulki a farkon shekarar 2021, ya ziyarci birnin Beijing da nufin tattaunawa da mahukun kasar China kan batutuwa da suka zama karfen kafa kuma ake kai ruwa rana a kansu tsakanin China da Amurka.
0 Comments