Majalisar Ɗinkin Duniya Zata Dakatar Da Kai Tallafin Abinci Ƙasar Habasha (Ethiopia)

 


Karkata akalar abincin da majalisar Ɗinkin Duniya ke kaiwa ƙasar ta Habasha ya jawo za a dakatar da basu tallafin kamar yadda hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar.


Wannan mataki dai ya fito ne acikin wata takardar sanarwa da hukumar ta fitar. 


Sai dai hukumar ta ce matakin bai shafi tallafin da take bayarwa na yaƙi da cutar tamowa ba, da kuma wanda take baiwa mata masu juna biyu ba, hakanan shi ma tallafin da take baiwa ɗalibai wannan mataki bai shafe shi ba.


Irin wannan matsala ta juya akalar tallafin abinci yasa Amurka ta janye tallafin abincin da take baiwa ƙasar ta Habasha.


Ana ƙiyasta cewa dai cire wannan tallafi zai shafi aƙalla sama da mutum miliyan 20 na al'ummar ƙasar da ke fama da yunwa sakamakon yaƙe yaƙen da ake fama dashi.


Sama da mutum miliyan biyar ne dai na al'ummar ƙasar ke gudun hijira a ƙasashen ƙetare.

Post a Comment

0 Comments