Hukumar ‘Bloomberg’ ta Amurka ta bayyana cewa, tsarin biyan kudi na kasashen Afirka da zai bai wa kasashen nahiyar damar yin kasuwanci a tsakaninsu, ta hanyar amfani da kudadensu, na kara samun karɓuwa.
Hukumar ta yi nuni a cikin wani rahoto da ta fitar cewa, bankin shigo da kayayyaki na Afirka yana sa ran kasashe 15 zuwa 20 na Afirka za su shiga cikin tsarin biyan kudi da kudaden kasashensu, maimakon yin amfani da dalar Amurka.
Shugaban bankin na Afirka Benedict Orama ya bayyana a wata hira da aka yi da shi gabanin taron shekara-shekara na bankin a kasar Ghana cewa, dandalin ya fara gudanar da harkokin kasuwanci da kasashe tara da suka sanya hannu kan yarjejeniyar ya zuwa yanzu.
Hukumar ta yi nuni da cewa a karshen shekarar 2020, jimillar kadarorin bankin da kuma lamunin da ya samu sun kai dala biliyan 21.5, kuma kudaden masu hannun jari sun kai dala biliyan 3.4.
A cewar hukumar, ba Afirka kadai ba ne ke neman hanyoyin karya dogaro da kudin Amurka, an yi ta kokarin rage dala a kasuwannin da ke tasowa, ciki har da kokarin da Indiya ke yi na kawar da kasuwanci ta hanyar kudi.
Hukumar ta bayyana cewa, kasar Sin ta yi wasa da ra'ayin asusun ba da lamuni na Asiya, yayin da kasashen Brazil da Argentina suka sanar da wani shiri na samar da kudin bai daya da ake kira "Sur".
0 Comments