Wato wuyar da aka sha a zamanin Abacha ba karama ba ce. Ko mu da muke yara a lokacin mun santa. A zamanin Abacha idan bokitin robar gidanku ya fashe to sai ka yi sati a layin mai liki. A lokacin ake bin layin nikan tuwon wani satin. A lokacin ake faci da dinki maje-gaba.
A zamanin Abacha ne masu kosai suke tsintar leda su wanke a sake zuba wani a ciki. A lokacin akai ciniki tsofaffin takalma silifas a Kasuwar Kurmi. Idan kana da dan-Madina to ku masu kudi ne! A zamanin Abacha ake layin siyan kalanzir kuma a lokacin aka saba da layin shan man fetur. A lokacin laccarori suke acaba.
Mallam an sha wuya a zamanin Abacha. Kada Allah ya maimaitawa Najeriya irinsa.
Haka Yake Tarihi Bashida Tausayi.
Karin Haske Akan Wannan
A Zamani Mulki Marigayi Janar Sani Abacha Wanda ya fara daga Ranar 17 Ga Watan Nuwamba 1993 zuwa 8 Ga Watan Yuni 1998, tabbas Talakawan Najeriya sun dandana kudarsu, A lokacin A Darajar kudi irinta wancan lokaci saida Galan guda na Man Fetur Yakai Naira N1000, Saida ya zamo gidajen man fetur basa iya sauke mai sai da taimakon sojoji, idan kaje layi A gidan man fetur sojoji ne suke kula da masu layi Neman man fetur. Saboda kada ayi tashin hankali.
A lokacin mulkin Janar Sani Abacha akwai lokacin da mutum zai nemi man fetur din da kudinsa ya Rasa. A lokacin Mutane har kwanakin suke A layin mai kafin su samu, A zamanin kimar sojoji ta zube wajen karbar cin hanci a gidan mai, Kaga ana kokawa da soja A gidan Mai, wannan Abune da ya zama ruwan dare.
A Zamanin Janar Sani Abacha Mafi karanci Albashi shi ne N800, Duk Da Kudi Sunada Daraja A Lokacin Amma Ko Kusa Basa isar Ma'aikaci fiye da Yanzu, to N800 din ma Sai a shafe Wata Uku Ba a Biya Ma'aikata ba daga matakin jiha har zuwa na tarayya.
A zamanin mulkin sani Abacha Dinka Shadda Yafi Karfin Talaka Nesa ba kusa ba.
Wasu Zasu iya cewa A Zamanin Mulkin Janar Sani Abacha An Sami Zaman Lafiya A Najeriya Babu Tashin Bama-bamai.
Kwarai Kuwa Amma Ba Haka Bane, A Zamanin Mulkin Janar Sani Abacha An Sami Tashin Bama-bamai Wanda Wannan shine Karon Farko na ganin Tashin bama-bamai A Tarihin Rayuwar Wasu Mutane a kasar..
Da farko A Shekarar 1994 (Na Manta Ranar Da Watan)
1, A Gidan, Dan Suleiman, Air Commodore mai ritaya, dake Victoria Islan Lagos an kai masa harin bam Kuma Sanadiyar Tashin Bom Din Ya Halaka.
2, 1995, Wani bam ya tashi a filin wasa na garin Ilorin, wurin da aka kaddamar da shirin tallafawa iyali (FSP) reshen jihar Kwara. Wasu yaran makaranta da ba su ji ba ba su gani ba sun rasa rayukansu.
3, A Ranar 18 Ga Watan Janairu 1996, Wani bam ya tashi a otal din Durbar mai taurari biyar da ke Kaduna, inda ya kashe wani mutum tare da raunata Wata mace manajan otal din.
4, A Ranar 17 Ga Watan Janairu 1996 wani hatsarin jirgin sama a Kano ya yi hadari inda Wanda Ya kashe Ibrahim Abacha (Dan Janar Sani Abacha) da wasu mutane. A Ranar 20 Ga Watan Janairu 1996, Wani bam ya sake tashi a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, A lokacin isowar manyan baki da ke tururuwa zuwa Kano domin jajantawa iyalan Abacha.
5, A Ranar 15 Ga Watan Nuwamba 1996 Wani bam da ya tashi a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja ya yi sanadin mutuwar Dr. Sola Omatsola, babban jami’in tsaro na filin jirgin. Wannan lamari dai yazo Ne A lokacin da aka fara kai hare-haren bama-bamai a otal-otal da wuraren sojoji da sauran wurare a Legas.
6, A Ranar 16 ga Disamba 1996 Wani Abin fashewa ya fashe a kan ayarin motocin Gwamnan Mulkin soja jihar Legas, Mohammed Buba Marwa.
7, 18 ga Disamba 1996 Bam ya tashi a Sakatariyar Gwamnati, kusa da ofishin gudanarwar A Lagas.
8, 7 ga Janairu 1997 Wani fashewar bam ya yi sanadin mutuwar wasu 'yan kasar da ba su ji ba ba su gani ba A Lagas.
9, 7 ga Mayu 1997 Wani bam ya tashi a Oko-Oba, wurin da aka yi kaurin suna a Legas. Wannan lamari Shi ne na karshe ya yi sanadin jikkatar mutane da dama ciki har da jami'an soji.
Wadannan Hare-haren kusan duk sun Faru A Lagas, kuma an ce lamarin ya dagula harkokin kasuwanci da tattalin arziki da zamantakewa da kuma siyasar kasar baki daya.
Kuma A Lokacin ne A Jihohi irinsu Kano Aka soma Ganin Ana Gwada Mutane Da Na'urar (Bomb Ditective 💣) Idan zasu shiga Ma'aikatun Gwamnati Kamar Gidan Murtala. A lokacin Mutane Su na Mamaki da jin Tsoro tare da Fargaba Domin Basu taba Ganin Irin Haka Ya Faru ba A Tarihin Rayuwar su.
Daga @Aliyu dahiru
Madogara: Mujallar Tell. 6, Fabrairu 5, 1996
Guardian, Disamba 22, 1996
© IFRA-Nijeriya, 1997
0 Comments