A TARIHIN MUSULUNCI ME YA FARU A IRIN WANNAN RANAR?

 


Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai


“To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo kama daga ilmi, to ka ce: “Ku zo mu kirayi ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa’an nan kuma mu kankantar da kai, sa’an nan kuma mu sanya la’anar Allah a kan makaryata”. (Suratu Al-Imrana 3:61)

Kusan karshe-karshen rayuwar Ma’aiki (s.a.w.a), sakamakon irin nasarar da Musulunci ya samu kuma yake ci gaba da samu, da dama daga dauloli da kasashen da suke kewaye da daular Musulunci sun nufo Madina don mika wuya da amsa kiran Manzo (Musulunci), sai dai duk da haka wasu daga cikin kasashe da kabilun ba su musulunta ba don haka Ma’aiki (s.a.w.a) ya aike musu da wasikun gayyata zuwa Musulunci.


Daga cikin al’ummar da Ma’aikin (s.a.w.a) ya aike musu da irin wannan goron gayyata har da kiristocin Najran (da ke kasar Yemen). A cikin wannan wasika da Manzon Allah (s.a.w.a) ya aike wa babban fadan Najran wato Abu Haris bn Alkama yana cewa:

"…..bayan haka, ina kiranku zuwa ga bautan Allah maimakon bautan bayinSa, ina kiranku zuwa ga mika kai ga Allah maimakon mika kai ga bayi, idan ba ku karbi wannan kira nawa ba, to ku amince da bayar da jizyah ga gwamnatin Musulunci in kuwa ba haka ba to ku shirya wa yaki. Wassalam.”.



Lokacin da wasikar Ma’aiki (s.a.w.a) ta shiga hannun mutanen Najran din sai manyansu suka taru don tattaunawa kan wasikar da kuma aiwatar da abin da ya dace. Bayan tattaunawa, da kuma bayanin da wasu suka yi na cewa lalle Allah Ya yi alkawari wa Annabi Ibrahim cewa zai tayar da wani annabi cikin zuriyar dansa Isma’il, don haka yana da kyau a tura tawaga wacce za ta tafi wajen Ma’aiki (s.a.w.a) don tattaunawa da shi da kuma dubi cikin lamurransa da kuma yanayinsa. Don haka aka shirya tawaga karkashin jagorancin babban malamin kiristan garin da sauran manyan malamai da za su tafi Madina don ganawa da Ma’aiki (s.a.w.a).



Lokacin da wannan tawaga ta iso Madina, sai suka canza tufafin da ke jikinsu suka sanya tufafi na alfahari na hariri da zobbunan zinare da giciye a wuyayensu suka nufi masallacin Ma’aiki don ganawa da shi. Ko da suka iso wajen Ma’aiki sai ya juya musu baya, ya ki saurarensu. Ganin haka sai suka fita suka nufi wajen wasu sahabbai suna neman shawararsu kan me ya kamata su yi ganin Manzo ya ki saurarensu. Wadannan sahabbai dai ba su san me ye abin yi ba, sai da suka zo wajen Imam Ali (a.s) (wata ruwayar kuma ta ce su kansu wadannan sahabbai ne suka tambayi Ali kan mene ne ya kamata su yi) inda shi ne ya ce musu su cire wadannan tufafi da suka sa su sanya tufafinsu na malamai su tafi wajen Ma’aikin zai saurare su. Bayan da suka yi hakan kuwa, sai Ma’aiki (s.a.w.a) ya tarbe su da yin maraba da su yana mai cewa: “Na rantse da Sarkin da Ya aiko ni a matsayin ManzonSa, lokacin da suka zo na farko, na gansu ne tare da Shaidan”.


Bayan gabatar musu da addinin Musulunci, kiristocin sun tambaye cewa: ‘Me za ka ce kan Isa dan Maryam?’ sai ya ce musu:

“Shi bawan Allah ne kuma ManzonSa”.

Su kuma kiristocin suka ce a'a shi kaza da kaza ne (wato suka fadi akidarsu kan Annabi Isa (a.s) shi kuma Ma'aiki (s.a.w.a) yana amsa musu da mahanga ta Musulunci, har aka saukar masa da ayar: "Lalle ne misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adamu ne, (Allah) Ya halitta shi daga turbaya, sa'an nan kuma Ya ce masa: "Ka kasance", sai ya kasance". (Suratu Al-Imrana 3:59)

Bayan wasu tambayoyi da amsoshin da Manzo (s.a.w.a) ya ba su, wadannan kiristoci sun ki amincewa su karbi Musulunci, duk kuwa da tabbatattun hujjoji da Ma’aiki ya kafa musu.

Don haka sai Allah Madaukakin Sarki Ya saukar da ayar mubahala da muka kawo a sama, wato:

“To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo kama daga ilmi, to ka ce: “Ku zo mu kirayi ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa’an nan kuma mu kankantar da kai, sa’an nan kuma mu sanya la’anar Allah a kan makaryata”

Bayan saukar wannan aya Manzon Allah (s.a.w.a) ya gabatar wa kiristocin da tayin yin mubahala (wato tsinuwa tsakanin da neman Allah Ya la’anci makaryaci).


Bayan tattaunawa tsakaninsu, kiristocin sun amince da wannan tayi na Manzo, inda suka tsayar cewa a taru a rana ta gaba don mubahalar. To amma sai babbansu Abu Haris ya ce musu ku sanya ido sosai idan har Muhammadu ya fito mubahalar tare da 'ya'yayensa da Ahlulbaitinsa kada ku yarda ku yi mubahalar, amma idan ya zo ne da sahabbansa da mabiyansa to ku yarda ku yi mubahalar da shi.

Tun da sanyi safiyar ranar 24 ga watan Zul Hajji, Manzon Allah (s.a.w.a) ya bukaci sahabbansa da su shirya wajen da za a yi mubahalar a wajen gari inda shi da mutanen gidansa za a su zauna. Ko da lokaci ya yi sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya fito tare da iyalan gidansa, wato yana dauke da Imam Husain (a.s), yana rike da hannun Imam Hasan (a.s) Nana Fatima da Imam Ali (a.s) suna biye da shi, Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce musu: "Idan kun ji na yi addu'a ku ce min amin". Koda ganin Ma'aiki da iyalan gidansa, sai babban kiristocin ya tambaya cewa: su wane ne wadannan? Sai aka ce masa: wancan na bayan Muhamamdu dan baffansa ne kuma mijin 'yarsa, wadancan yaran kuma 'ya'yan 'yarsa ne ita kuma wancan 'yarsa ce, wacce tafi soyuwa a gare shi sama da kowa kuma abin kaunarsa. Don haka sai wannan babban malamin kirista ya ce wa mabiyansa:

"Ya ku nasara (kiristoci)! Lalle ni na ga wasu fuskoki da idan suka roki Allah da Ya kawar da wani dutse daga inda ya ke, lalle zai kawar da shi da su, don haka kada ku yi mubahala da su sai ku halaka, kuma babu wani kirista da zai saura a bayan kasa har zuwa tashin kiyama".

Don haka sai suka ce wa Manzon Allah (s.a.w.a): "Ya Abal Kasim, lalle mu ba za mu yi mubahala da kai ba, mu barka a kan addininka kai ma ka bar mu a kan namu".

Sai ya ce musu: "To idan ba za ku yi mubahala ba, to ku musulunta, sai ku sami duk abin da musulmi suke samu, da kuma wani abin da ya hau kan musulmi"

Amma sai suka ki amincewa don haka sai Ma'aiki (s.a.w.a) ya ce musu: "To ku shirya wa yaki". Sai suka ce: Lalle ba mu da karfin yaki da larabawa, sai dai kawai mu yi sulhu tsakaninmu cewa ba za ka yake mu ba, kuma ba za ka kawar da mu daga addininmu ba, mu kuma kowace shekara za mu dinga ba ka kayayyakin ado dubu biyu: dubu guda a Safar, dubu gudan kuma a Rajab da kuma garkuwa guda talatin na bakin karfe".

Don haka sai Ma'aiki (s.a.w.a) ya amince ya yi sulhu da su yana mai cewa:

"Na rantse da wanda rai na ke hannunSa, da mutanen Najran sun yi mubahala da mu, da an mayar da su birrai da aladu, da an musu ruwan wuta, da kuma an halaka mutanen Najran da dukkan abin da ke ciki hattta tsuntsayen da ke kan bishiyoyi".

Wannan dai shi ne labarin mubahala da abin da ya faru wanda mabiya Ahlulbaiti (a.s) suke nuna farin cikinsu da yin bukukuwa a duk lokacin da wannan rana ta zagayo saboda abin da ta kumsa na nuna falalar Ahlulbaiti (Ashab al-Kisa) a kan sauran sahabbai, kamar yadda Zamakshari cikin Tafsirinsa na Al-Kashshaf yayin da yake magana kan wannan aya ta mubahala ya ke cewa: "Wannan aya dalili ne mai karfin da ya wuce kowanne kan falala da fifikon As'hab al-Kisa" (wato Muhammad, Ali, Fatima, Hasan da Husain - a.s-).

Wannan magana babu kokwanto cikinta don kuwa hatta sahabban Ma'aikin sun fahimci haka shi ya sa ma wasu daga cikinsu suka yi fatan da da su ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya fita don yin mubahalar.

A takaice dai wannan aya ta mubahala da shi kansa abin da ya faru a wajen mubahala yana nuni da wasu muhimman al'amurra da suka hada da: nuna irin matsayin da Imam Ali (a.s) mai dakinsa Fatima al-Zahra da 'ya'yansa Hasan da Husain wajen kare addinin Musulunci da tabbatar da gaskiyarsa da kuma rashin ingancin sauran addinai. Kamar yadda ayar tana nuni da matsayin Amirul Muminina (a.s) da kuma halifancinsa bayan Ma'aiki da kuma cewa babu wani da zai aiwatar da aikin Ma'aiki (s.a.w.a) a bayansa in ba shi ba. Saboda idan aka duba ayar za a ga cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya zo ne da Ali (a.s) a matsayin ( ﻭَﺃَﻧﻔُﺴَﻨَﺎ ) "Kanmu", don a fili yake cewa Ali (a.s) ba zai shiga cikin "'ya'yanmu" da yazo cikin ayar ko kuma "matanmu" ba, inda kawai zai iya shiga shi ne wajen "kanmu", wanda hakan na nuni da cewa Manzon Allah (s.a.w.a) yana daukan Ali (a.s) ne a matsayin shi kansa, wato shi ne zai iya zama a kujeransa a lokacin da ba ya nan, wanda hakan na nuni da fifikonsa a kan sauran sahabbai.

Kamar yadda kuma Alkur'ani da kansa yake nuni da cewa Hasan da Husain (a.s) 'ya'yan Ma'aiki ne (s.a.w.a) da suk fi sauran 'ya'ya. Sannan Fatima al-Zahra (a.s) kuma a matsayinta na macen da tafi sauran mata ciki kuwa har da matan Ma'aiki (s.a.w.a) don kuwa idan ba haka ba da ya zo da su wajen mubahalar.

A takaice dai wadannan mutane da Manzo (s.a.w.a) ya zo da su su ne suka fi kowa daukaka. Don haka ne mabiya Ahlulbaiti (a.s) suke gudanar da bukukuwa a duk lokacin da wannan rana ta zagayo.

Allah Ya maimaita mana.


- Bin Yaqoub Katsina

Post a Comment

0 Comments