Al'ummar Musulmi Sun Gudanarda Gangamin Allah Wadai Da Cin Zarafin Qur'ani A Indonesia.



- Freedom Fighters Ng

Suma al'ummar musulmin kasar Indonesia ba a barsu a baya ba wajen nuna rashin yarda da cin mutuncin Qur'ani mai tsarki da akayi a kasar Sweden.


Al'ummar Musulmi da yawa ne suka taru a birnin Jakarta domin gabatar da gangamin  Allah wadai da mummunar aika aikar kona Qur'ani a gaban wani masallaci a Stockholm a ranar 28 ga watan yuni da ya gabata.


Mahalarta gangamin sun karanta wani bangare na Qur'ani mai girma a wajen gangamin, suna dauke da takardu masu dauke da rubutu.


Masu gangamin sun bayyana cewa " Da wannan gangamin namu muna son mu nuna ma al'umma cewa Qur'ani littafi ne mai tsarki a wajen musulmi, dan haka ba zaiyiwu a kona ko yaga kurni ba saboda 'yancin fadin albarkacin baki (Freedom Of Speech)".


Wani la'ananne dan shekara 37 mai suna Salwan Momika ne ya jagoranci kona Qur'anin a lokacin da suka gabatar da wata zanga zanga a kasar ta Sweden.


Wannan aika aikar dai ta harzuka musulmi a fadin duniya inda al'ummar musulmi suke ta gabatar da gangami tare da jan kunnen dukkanin masu irin wannan aika aika.

Post a Comment

0 Comments