Ambaliyar Ruwa Ta Raba Mutum 500 Da Muhallansu, Anyi Asarar Dabbobi A Jihar Gombe.

 


A sakamakon ruwan da aka tafka kamar da bakin ƙwarya a jihar Gombe da ke arewacin Najeriya, an samu ambaliyar ruwa a Dogon Ruwa dake ƙaramar hukumar Kaltungo.


Wannan ibtila'i dai ya share aƙalla gidaje 100, wanda yabar aƙalla mutum 500 babu muhalli.


A lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Punch shugaban unguwar da wannan ibtila'i ya auku ya bayyana cewa " bayan asarar gidaje anyi asarar dabbobi har goma sha biyar (15) wanda suka haɗa da Akuyoyi da Tinkiyoyi."


Ya ƙara da cewa al'ummar Dogon Ruwa suna neman gwamnati ta taimaka masu da sutura da kayan abinci, yace dai sun miƙa ƙorafinsu Ƙaramar Hukuma domin suna cikin mawuyacin yanayi.


Ya bayyana cewa sun rasa Gidaje 100 tare da dabbobi 15, a halin yanzu dai kusan mutum ɗari biyar ne suka rasa muhalli, babban abinda yafi damun su a halin yanzu shine rashin sutura da kayan abinci, daga ƙarshe dai ya bayyana cewa asarar da sukayi a dalilin wannan ambaliyar Ruwa ta Miliyoyin kuɗaɗe ce.

Post a Comment

0 Comments