Su ma kansu wadannan mutanen (yammacin duniya) sun yi wani tunani, suka ce gaskiyar magana, yanzu Musulunci yana dagowa. To kuma yana firgita su, dagowar Musuluncin, kowane yana kokarin ya fassara Musuluncin ta yadda yake ganin shi ne ya fi zama daidai.
To su Yamma, suka ce suna bukatar fassarar da ba zai zama ya cuci muradinsu ba (interest dinsu kenan), suna son fassarar Musulunci ne wanda zai yi daidai da muradinsu. To, suka ce, sai suka raba Musulmi kashi uku; akwai wadanda suka kira su da masu tsattsauran ra’ayi, akwai wadanda suka kira su matsakaita, akwai wadanda suka kira su na al’ada.
Bari na muku da Ingilishi, akwai ‘extremist’, akwai ‘moderate’ akwai ‘traditionalist. Su ‘traditionalist’ su ne wadanda suka dauka addini shi ne sallah da zikirori da karatu da sauransu. ‘Extremist’ kuma su ne suka ce lallai sai a sauya nizamin a koma addini. To ‘Moderate’ kuma su ne ‘yan baina-baina, su Yammatawa ne a tunani, amma Musulmi ne a addini, amma tunaninsu ya yammace, saboda haka su suna ganin su Musulmi ne, amma dai za a tafi tare da Yamma ne.
Suka ce to su ya kamata su yi la’alakari da kowanne daga cikin ukun nan. Na farko, suka ce shi ‘traditional’ da ka gani, wanda yake shi bai da hadari, shi yana da kyau a bar shi a yadda yake, kar a tsokano shi, a kyale shi ya yi ta zikirinsa, shi ka ga an huta kenan. Shi kuma Moderate, shi ya kamata a karfafa shi a tafi tare da shi, saboda shi a tunaninsa Bayammace ne, amma shi a addininsa ne Musulmi, to da shi za a tafi. Amma ka ga wannan mai tsattsauran ra'ay’n, to lallai a yi maganinsa.
Sai suka ce, to amma fa a yi saufa-saufa fa, don ka ga shi Batsakaice din nan, ‘moderate’ kenan, suka ce to ko shi ma fa yana tsaka mai wuya ne, wadannan masu tsattsauran ra’ayi suna ganinshi a matsayin ya bar addini ya Yammace, su kuma ‘traditonalist’ suna ganin shi ma ba addini yake ba, saboda haka yana tsaka mai wuya ne, yana kokarin ya nuna ma dukkansu shi Musulmi ne, to idan aka matsa masa, ‘extremist’ suna iya yin fada da shi.
Sannan kuma sai suka ce, su ma ‘traditonalist’ kar ka dauke su ‘for granted’, saboda idan aka taba wani abu, suka ga cewa ana fada da addininsu ne, su ma za su koma su zama ‘Extremist’. Shi ma ‘moderate’ din nan ka yi a hankali da shi, domin idan ya an taba addini shi ma yana birkicewa.
To zan fada muku karshen maganar da suka yi, suka ce abin da ya kamata shi ne su ma su yi ‘extremist’ dinsu. To wannan shi ne abin da muke fama da shi yanzu. Suka kirkiro nasu. Duk wadannan su DAESH ne, ISIS ne, Boko Haram, su Shabab duk su suka kirkiro, duk kirkiran Amurka ne. Duk inda ka ji ana wadannan bala’in da sunan addinin Musulunci, to su suka kirkiro.
To amma ya faskare su su kirkiro Shi’a, sun kasa kirkiran Shi’a. Amma sun dan fara yi. Kun san akwai maganar Sayyid Khamene’i da ya yi maganar Shi’ar London ko? Kwanan nan ma shi Sayyid Ra’isi yace akwai kuma Sunnati Amerika. Yanzu akwai Shi’atu London, akwai Sunnatu Amerika. Wato akwai Shi’a kirkiran London, akwai kuma Sunnah kirkiran Ingila, saboda haka a yi hattara da irin wadannan. Duk ba wani abu bane, illa suna kokari ne su canza ma mutane Afkar dinsu. Fikira din nan shi ne.
0 Comments