An karbo Daga Imamu Rida (as) yana cewa:"bayan an haifi Husain (as) Manzon Allah (s) ya nemi Asma'u ta kawo masa dansa Imamu Husaini (as) sai ta Kai masa yana lullube a cikin farin mayafi sai ya Yi Kiran sallah a kunnensa na dama,ya yi ikama a kunnensa na hagu."(Littafin Maqtal na Kwarizimiy 2/215).
An rawaito daga Shaikhus Saduuq yace:"a sadda aka haifi Husaini (as) Jibrilu ya zo daga sama tare da Mala'iku dubu goma suka taya Manzon Allah (s) murnar haihuwarsa."(Amaliy na Shaikh Saduok 118:babi na 27,Hadisi na 8).
Ya zo a wata ruwayar kuma bayan haihuwar Imamu Husaini (as) tawagogin Mala'iku sun rika zuwa suna wa Manzon Allah (s) murnar haihuwarsa.Imamu Ali (as) yana cewa:"Mala'iku dubu 24 ne suka zo Taya Manzon Allah (s) murnar haihuwar Imamu Husaini (as).
Bayan haihuwar Imamu Husaini (as),Mala'ika Jibrilu (as) ya zo wajen Manzon Allah (s) yana cewa da shi:"Hakika Mahaliccinka Yana gaida kai,sannan ya ce Hakika matsayin Ali a wajenka kamar matsayin Haruna ne a wajen Musa don haka ka sanyawa karamin dansa (Husaini) da "Shubairu"a yarenka Larabci yana nufin "Husain"."(Littafin Ra'iatil khalk maqtali Shaikh Ra'isi page 46).
A ranar uku ga watan Sha'aban mai albarka na shekara ta hudu bayan hijira aka yi wa Manzon Allah (s.a.w.a) albishir da haihuwar Husaini (a.s.). Don haka sai ya gaggauta tafiya gidan Ali da Zahara (a.s.), ya ce wa Asma'u bin Umais: "Asma'u kawo min dana." Sai Asma'u ta kawo wa Manzo shi dauke a farin zane. Sai Manzo ya yi murna da ganinsa, ya rungume shi, sannan ya kira salla a kunnensa na dama, ya kuma yi ikama a na hagu, sannan ya dora shi a cinyarsa sai aka ga yana kuka. Sai Asma'you, cikin mamaki, ta tambaye shi, cewa: "Wa kakewa kuka?" Sai Manzo (s.a.w.a) yace: "Dan nan nawa." Sai Asma'u ta ce: "Yanzun nan aka haife shi." Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce:
"Ya Asma'u!, wata azzalumar kungiyar karkatacciya ce za ta kashe shi a bayana, Allah ba Zai hada su da cetona ba".
SANNAN SAI YA CE:
"Ya Asma'u! Kar ki fada wa Fatima wannan labari, domin ba ta dade da haihuwarsa ba (1)".
Sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya sami sako daga Allah Madaukaki game da sunan abin haihuwarsa mai daraja; sai ya waiwayi Ali (a.s.) ya ce: "Ka sa masa suna Husaini".
MATSAYIN IMAM HUSAINI (AS)
Hakika Abu Abdullahi al-Husain (a.s.) na da babban matsayi. Bayan ayoyin Alkur'ani da suka ambaci matsayinsa cikin matsayin Ahlulbaiti (a.s.), wadanda muka ambata a baya, kamar su Ayar Tsarkakewa, Ayar Mubahala, Ayar Kauna da sauransu; akwai hadisan Annabi masu yawa da ke nuna girman matsayinsa da daukakar darajarsa. Daga cikin su akwai:
1- Abin da ya zo cikin Sahih al-Tirmizi cewa: Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Husaini daga gare ni yake, ni kuma daga gare shi nake. Allah Ya so wanda ya so Husaini. Husaini jika ne daga cikin jikoki(2).
2- An ruwaito daga Salman al-Farisi, ya ce: na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: "Hasan da Husaini 'ya'yana ne, wanda ya so su ya so ni, wanda kuma ya so ni Allah zai so shi, wanda kuwa Allah Ya so zai shigar da shi Aljanna. Kuma wanda ya fusata su ya fusata ni, wanda kuma ya fusata ni Allah zai yi fushi da shi, wanda kuwa Allah Ya yi fushi da shi zai shigar da shi wuta(3)".
3- An ruwaito daga Ali bin Husaini daga babansa, daga kakansa (a.s.), cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya kama hannun Hasan da Husaini (a.s.) sannan ya ce: "Wanda ya so ni ya kuma so wadannan biyun da babansu da mamansu, zai kasance tare da ni ranar kiyama(4)".
- Freedom Fighters Ng
Daga Littafin ''Ashura a mahangar Kiristoci da masana a jiya da yau''
Na Yusuf Kabir.
09063281016.
Za mu ci gaba insha Allahu.
0 Comments