Bayan Watanni 11, Ƴan Sanda Masu Kula Da Sanya Hijabi Sun Dawo Bakin Aiki A Iran.

 



Su dai waɗannan jami'ai an dakatar da aikinsu ne tun watan satumba na shekarar da ta gabata, sakamakon zazzafar zanga-zangar da ta barke a kasar ta Iran sakamakon mutuwar wata matashiya mai suna Mahsa Amini a shekarar da ta gabata 2022.

Rundunar da ake kira a harshen farsi Gasht-e-Ershad, aikin su  shine kula da sanya sutura da ta dace da shiga ta ɗa'a da hijabi a faɗin ƙasar ta Iran.

Mai magana da yawun wannan runduna mai suna Sa'id Muntazarul Mahadi ya bayyana wa manema labarai cewa a ranar Lahadi 16 ga watan Yuli tawagar ƴan sandan ta dawo bakin aiki inda jami'an su suka bayyana akan tituna a ƙasa da kuma kan ababen hawa.

Aikin jami'an na farko shine gargaɗin waɗanɗa suka saɓa dokar yin shiga ta mutunci, idan kuma mutum bai ji gargaɗin ba sai akai shi gaban alƙali.

Idan baku manta ba dai a shekarar da ta gabata ne jami'an suka kama Mahsa Amini da laifin karya dokar hijabi inda daga baya ta mutu a hannun jami'an, wanda haka ya haifar da mummunar zanga zanga a ƙasar.

Sai dai hukumomin ƙasar ta Iran sun bayyana cewa kasashen yamma nada hannu a wannan zanga zangar da ta auku.

A sakamakon wannan zanga zangar dai jami'an tsaron ƙasar Iran da dama ne suka rasa rayukansu.

©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

0 Comments